ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lakurawa Sun Kashe Insfektan Ƴansanda Da Mutane 11 A Kebbi

by Abubakar Sulaiman
18 hours ago

Wani mummunan hari da ake zargin ƴan ta’addar ƙungiyar Mamudawa ko Lakurawa ne suka kai kan ƙauyukan Wawilaiyi da Kystu da ke Ƙaramar Hukumar Koko/Besse ta Jihar Kebbi ya yi sanadin mutuwar wani Insfektan ƴansanda tare da fararen hula guda 11.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga yankin ne a ranar Laraba, inda suka buɗe wuta ba ji ba gani tare da yin gumurzu da jami’an tsaro kafin su shiga yankunan da abin ya shafa.

Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya bayyana cewa insfektan ƴansandan ya rasa rayuwarsa ne yayin da yake fafatawa da maharan domin kare al’umma.

ADVERTISEMENT

Bayan kashe jami’in tsaron da fararen hula 11, ƴan ta’addar sun sanya wuta a gidajen mutane sannan suka kwashe kayan abinci daga shaguna, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan mazauna yankin tserewa zuwa maƙwabtan garuruwa domin neman mafaka da tsira da rayukansu.

An tura tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da ƴansanda da sojoji zuwa yankin da abin ya shafa domin dawo da kwanciyar hankali.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

Rundunar ta ƙaddamar da bincike tare da aikin kakkabe dazuzzukan da ke kewaye domin gano maharan da suka aikata wannan ta’asa.

Hukumomin tsaro sun yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba da haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen daƙile irin waɗannan hare-haren a nan gaba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto
  • Abubakar Sulaiman
    Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci
Manyan Labarai

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA
Manyan Labarai

An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

October 30, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.