Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata malamar makarantar firamare, Amina Hussaini, a gidanta da ke garin Kuru, cikin Ƙaramar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa, tare da neman kuɗin fansa naira miliyan 50 kafin su sake ta.
An ce maharan sun sace malamar ne a ranar Talata, lokacin da mijinta ba ya gida, bayan ya tafi Lafia, babban birnin jihar, kan wani aiki. ƴar uwarta, Suwaiba Abdullahi, ce ta tabbatar da lamarin ga manema labarai ta wayar tarho ranar Alhamis.
Suwaiba ta ce masu garkuwar sun tuntuɓi iyalanta bayan sace ta, inda suka buƙaci a biya naira miliyan 50 domin sakin ta. Ta bayyana cewa iyalan na cikin ruɗani kan yadda za su samo kuɗin, yayin da yunƙurin wani ɗan uwa na tattaunawa da masu garkuwar domin rage kuɗin fansar ya ci tura bayan sun katse kiran wayar.
Ta ƙara da cewa har yanzu Amina tana hannun masu garkuwar, kuma an kai rahoton sace ta ga ƴansanda. Iyalanta sun yi kira ga hukumomin tsaro, Gwamnatin Jihar Nasarawa da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wajen tabbatar da sakin ta cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani sharaɗi ba.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya ce shi ma ya ga rahotannin sace malamar a kafafen sada zumunta, kuma zai gudanar da bincike domin samun ƙarin bayani kafin ya yi magana kan lamarin.














