Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta yi kira ga Gwamna Abdullahi Sule da ya gaggauta daukar matakin shawo kan matsalolin da suka addabi babban asibitin gwamnatin jihar da ke karamar hukumar Nasarawa.
Haka kuma, ‘yan majalisar sun bukaci a gaggauta tura karin ma’aikatan lafiya da samar da muhimman kayan aiki domin dawo da ayyukan asibitin yadda ya kamata.A zaman majalisar da aka gudanar a ranar Laraba a Lafia, Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Danladi Jatau, ne ya gabatar da kudurin majalisar bayan wata bukata ta musamman da Hon. Hajarat Danyaro (APC-Nasarawa ta Tsakiya) ta gabatar kan halin da asibitin ke ciki.
Majalisar ta kuduri aniyar bukatar Ma’aikatar Lafiya ta Jiha da Hukumar Kula da Asibitoci (Hospitals Management Board) su gaggauta tura karin likitoci da ma’aikatan jinya zuwa babban asibitin da ke karamar hukumar Nasarawa.Haka kuma, majalisar ta bukaci gwamnati ta inganta kayayyakin aiki da gine-ginen dukkan manyan asibitocin jihar domin inganta harkokin kiwon lafiya a matakin kananan hukumomi.
Da take bayyana tsananin matsalar, Hon. Danyaro ta ce asibitin na cikin wani hali da ke barazana ga lafiyar al’umma, inda ta bayyana cewa a halin yanzu likita guda daya da ma’aikaciyar jinya daya ne kawai ke kula da marasa lafiya har guda 30 a lokaci guda.
Ta kuma nuna damuwa kan rashin muhimman abubuwan more rayuwa a asibitin, inda ta ce marasa lafiya kan tilasta wa kansu samar da ruwan da za su yi amfani da shi sakamakon lalacewar kayayyakin more rayuwa da rashin tsafta.
A cewarta, duk kokarin da aka yi na sanar da Hukumar Kula da Asibitoci halin da ake ciki bai haifar da wani sakamako ba, lamarin da ya sa ta bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a asibitin.
Ta kuma bukaci gwamnati ta mayar da wasu kwararrun ma’aikatan lafiya da suka fito daga yankin zuwa asibitin, inda ta ba da shawarar a tura akalla likitoci uku da ma’aikatan jinya goma domin yi wa al’ummar yankin hidima.
Da suke goyon bayan kudurin, ‘yan majalisa ciki har da Hon. Yusuf Aliyu Chunbaya da Rt. Hon. Abel Yakubu Bala sun jaddada cewa majalisar ba za ta yi shiru kan tabarbarewar cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a a fadin jihar ba.
A karshe, Shugaban Majalisar ya umarci Magatakardar Majalisar, Mista Ibrahim Abdulazeez Musa, da ya aika da kudurin ga Gwamna Abdullahi Sule domin daukar matakin gaggawa na bangaren zartarwa.














