Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yanke hukunci na ƙarshe kan ɗimbin ƙorafe-ƙorafen da aka shigar gabanta dangane da jerin sunayen ƴan takarar babban zaɓen 2027, inda ta amince da tabbatar da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamna a Jihar Gombe, yayin da ta yi watsi da roƙon Ladi Adebutu na Jihar Ogun da kuma Aminu Gwarzo na Jihar Kano.
A wata sanarwa da Babban Kwamishinan Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe na hukumar, Mohammed Haruna, ya fitar a birnin Tarayya Abuja, ya bayyana cewa hukumar ta duba tare da amincewa da korafe-korafe 66, yayin da ta yi watsi da wasu 64 bayan ta gano cewa ba su cika sharaɗin doka ko kuma ba su da ingancin da ya kamata.
Matsayin Ƴan Takarar da Lamarin ya shafa
Majiyoyi daga shalƙwatar hukumar sun tabbatar da cewa an amince da Farfesa Isa Ali Pantami tare da tabbatar da takararsa ta gwamna a Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, biyo bayan binciken da aka gudanar kan ƙorafin da jam’iyyar ta shigar.
A ɓangaren Ladi Adebutu, ɗan takarar gwamnan PDP a Jihar Ogun, majiyar ta bayyana cewa an ƙi amincewa da ƙorafinsa ne saboda asali ba a haɗa sunansa cikin jerin sunayen ƴan takarar da jam’iyyar ta miƙa wa INEC ba tun da farko.
Haka ma a game da Aminu Gwarzo na Jihar Kano, hukumar ta bayyana cewa akwai wani umarnin wucin gadi daga Babbar Kotun Tarayya (Ex parte order) da ya hana INEC buga sunansa, inda ta jaddada cewa makomar takararsa za ta dogara ne kaɗai kan sakamakon shari’ar da ake gudanarwa a kotu.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa ta karɓi korafe-korafe 69 daga jam’iyyu 12 a jihohi 26 dangane da zaɓen gwamna, inda ƙorafe-ƙorafe 41 suka yi nasara aka amince da su, sannan 28 suka faɗi. Haka zalika, a matakin zaɓen ƴan majalisar dokokin jihohi, hukumar ta karɓi ƙorafe-korafe 61 daga jam’iyyu 11 a jihohi 11, inda aka amince da 25 aka kuma yi watsi da 36.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta fitar da sabon jerin sunayen da aka sabunta a shafinta na intanet domin bai wa jama’a da jam’iyyun siyasa damar ganin yadda lamarin yake. INEC ta kuma jaddada cewa dukkan matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tanadin Dokar Zaɓe da hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan game da tilas na gabatar da rajistar mambobin jam’iyyu.














