ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 30, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

by Abubakar Sulaiman
11 hours ago

Al’ummar Margi da ke Jihar Borno ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Babagana Zulum da su ƙara ƙaimi wajen kuɓutar da ɗalibai 78 da wani malami da aka yi garkuwa da su a garuruwan Mussa da Lassa, cikin Ƙaramar Hukumar Askira/Uba.

Al’ummar ta ce iyalan waɗanda aka sace na cikin damuwa tun bayan faruwar lamarin, yayin da yaran da malamin ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa.

Sakatare na al’ummar, Malla Gadzama, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis. Ya ce an sace ɗalibai 43 daga Mussa a ranar 15 ga Mayu, 2026, yayin da aka sace wasu ɗalibai 35 da malami guda daga wata makarantar sakandare da ke Lassa a ranar 26 ga Yuni, lokacin da suke shirin jarabawar ƙasa.

ADVERTISEMENT

Gadzama ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya tattara dukkan kayan aikin tsaro da bayanan sirri da ake da su, tare da tabbatar da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin ceto waɗanda aka sace. Ya kuma yi kira ga Gwamna Zulum da ya mayar da batun sakin yaran cikin abubuwan da gwamnatinsa ke ba fifiko, tare da samar da hanyar sadarwa da iyalan domin sanar da su sahihan bayanai kan halin da ake ciki ba tare da kawo cikas ga aikin ceto ba.

Al’ummar ta kuma buƙaci Sanata Ali Ndume da sauran wakilan yankin Askira/Uba da su yi amfani da matsayinsu wajen matsa wa hukumomi su ɗauki matakan da suka dace. Ta kuma nemi a ƙarfafa tsaro a makarantun da ke yankunan da ke fuskantar barazanar hare-hare, tare da samar da taimakon lafiya, na tunani da na ilimi ga yaran idan aka kuɓutar da su.

LABARAI MASU NASABA

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

Gadzama ya yi nuni da sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, wanda ya bayyana tsaro da walwalar jama’a a matsayin babban nauyin gwamnati. Ya ce al’ummar ba neman wata alfarma take yi ba, illa tana buƙatar gwamnati ta sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.

Ya buƙaci Tinubu, Zulum da hukumomin tsaro su ci gaba da ƙoƙarin ceto yaran da malamin har sai sun koma hannun iyalansu cikin ƙoshin lafiya.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

MASU ALAKA

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci
Manyan Labarai

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA
Manyan Labarai

An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

October 30, 2026
Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC
Manyan Labarai

Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC

October 30, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

October 30, 2026
An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

October 30, 2026
Majalisar Nasarawa Ta Buƙaci Gwamna Sule Ya Ɗauki Matakin Gaggawa Kan Babban Asibitin Jihar

Majalisar Nasarawa Ta Buƙaci Gwamna Sule Ya Ɗauki Matakin Gaggawa Kan Babban Asibitin Jihar

October 30, 2026
Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC

Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.