Karamin Dandalin Tattauna Hada-hadar Kudi Da Aka Bude A Kenya Ya Karkata Ga Batun Zuba Jari A Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya
An kaddamar da karamin dandalin tattauna batutuwan hada-hadar kudi na shekarar nan ta 2026 a kasar Kenya. Karamin dandalin na bana da aka bude a jiya Laraba a birnin Nairobin kasar Kenya, bisa taken "Gudanar da komai a bude da cimma moriyar bai daya: Gina sabon karsashi domin nasarar hadin gwiwar ‘Ziri daya da hanya daya’ mai matukar inganci", shi ne karon farko da yake gudana a nahiyar Afirka. Ya kuma gudana tare da babban dandalin na birnin Beijing. An hada tsakanin babban dandalin na birnin Beijing da na birnin Nairobi ta kafar bidiyo, inda mahalarta suka yi musayar raayoyi dangane da batutuwa da dama, ciki har da zuba jari a shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da hadin gwiwar samar da kudade, da hadin gwiwar hada-hadar kudade tsakanin kasa da kasa. Da yake tsokaci yayin zaman, memban majalisar ministocin kasar Kenya mai lura da harkokin kudi da tsara tattalin arziki John Mbadi Ng'ongo, ya ce shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta taimaka wa kasashen da suka shiga cikinta, da damar kyautata dinkewa waje guda, da ingiza harkokin cinikayya da zuba jari, da fadada kafofin bunkasa hada-hadar kudi. Kazalika, a cewar sa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, ta samar da zarafin tattara albarkatu domin manya ayyukan samar da ci gaba masu muhimmanci, da ingiza raba ilimi da musayar fasaha, da zurfafa bunkasar dunkulewar tattalin arzikin yankin. (Saminu Alhassan)



















