Bankin shige da fice na Sin ya sanar da nasarorin da ya samu a hadin gwiwar gina ayyuka masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kuma muhimman bangarorin hadin gwiwa a nan gaba.
Bankin ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin taro kan shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da aka yi a gefen taron shekara-shekara kan harkokin kudi na Sin.
Rahotanni sun bayyana cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, bankin na Sin ya bayar da rancen sama da yuan triliyan 7 ga ayyukan shawarar, wadanda suka shafi kasashe 130.
Yanzu haka, hadin gwiwar gina “Ziri Daya da Hanya Daya” ya shiga wani sabon mataki na ci gaba mai inganci. Shugaban bankin Chen Huaiyu ya ce, bankin zai ci gaba da inganta karfinsa na hadin gwiwar da aka saba kan ababen more rayuwa kamar layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa da makamashi, yayin da yake mayar da hankali kan fannoni kamar na makamashi mai tsafta da tattalin arziki na dijital, domin taimaka wa kasashe abokan huldar shawarar, kafa nasu tsarin masana’antu.
Ya kara da cewa, bankin zai ci gaba da hada hannu da Sin wajen bunkasa manyan ayyuka da ma shirin kyautata rayuwar jama’a mai lakabin “karami, mai kyau,” da gaggauta aiwatar da shirye-shiryen kare muhalli da hanyar siliki mai fasahar zamani da tallafa wa tsarin gargadin yanayi na MAZU a Afrika, domin bunkasa karfin karewa da magance ibtila’in yanayi. (Fa’iza Mustapha)














