A bana aka cika shekaru 70 da Sin da Afirka suka kulla huldar diflomasiyya, kuma ita ce shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka. Kwanan nan, sashen Asiya da Afirka na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG tare da hadin gwiwar tashar yada labarai ta
Lardin Hunan na CMG sun gabatar da bikin “Yawo a Sin-ziyarar Hunan”, inda suka gayyaci ‘yan jarida na manyan kafofin yada labarai daga Nijar, Ghana da sauransu, da masanan malamai da shahararrun masu yada labarai a yanar gizo su shiga biranen Changsha, da Shaoyang da Xiangxi, domin kara wa juna sani da ingiza musayar dabarun ci gaba.
Hunan babban lardi ne na noma. Tawagar ta ziyarci cibiyar binciken shinkafar da aka tagwaita ta Hunan, don fahimtar sakamakon aikin taimaka wa nahiyar Afirka bisa ayyukan shinkafar, tare da mai da hankali kan shirin hadin gwiwa na tabbatar da isasshen abinci ga kasashe masu tasowa. Sun kuma shiga manyan kamfanonin fasahohin zamani da dama, inda suka fahimci yadda kayayyakin injuna ke taimaka wa aikin gina ababen more rayuwa a Afirka, da kuma ganin yadda fasahar kirkire-kirkire ta zamani ke taka rawa wajen gyara tsarin masana’antu da kyautata rayuwar jama’a.
Samira lbrahim Sabou, wata shahararriyar mai yada labarai a shafin sada zumunta na Nijar, ta ce ta ga yadda Sin ke kokarin kirkirar mutum-mutumin inji iri daban-daban da bunkasa fasahohin zamani don bauta wa jama’a, da kyautata zaman rayuwarsu.(Amina Xu)














