Karuwar Da Tattalin Arzikin Sin Ya Samu A Dukkan Rubu’i 3 Na Farkon Bana Ya Zarce Hasashen Da Aka Yi
Bisa lissafi na farko-farko, alkaluman GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 10.71071 a rubu’i 3 na farkon bana, inda aka samu karuwar kaso 4.6 a mizanin shekara-shekara. Kafofin yada labarai na kasa da kasa kamar BBC da Reuters, sun gabatar da nasu sharhi masu take daban-daban kamar “Tattalin Arzikin Sin ya Karu a Q1-Q3” da “Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin daga Q1-Q3 ya Wuce Tsammani”… Bisa kididdiga, gudunmuwar da manyan masana’antu na kasar suka bayar ga tattalin arzikin ya karu da kaso 5.3 cikin rubu’i 3 na bana, yayin da sayayyar kayayyaki da na hidimomi ta karu da kaso 2.6. Galibin ma’aunan tattalin arziki sun samu ci gaba, lamarin da ke nuna juriya da kuzarin habakar tattalin arzikin Sin da ma jaddada matsayinsa na mai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya ga kasashe da yankuna 169, inda jimilar kayayyakin da ke shiga kasar da ma wadanda ke fita ta karu da kaso 18.8 a mizanin shekara-shekara cikin rubu’in 3. Baya ga haka, karuwar kayayyakin da kasar Sin take saya daga ketare ta ci gaba da zarce kaso 20 cikin dukkan rubu’in 3, wadda ke kara nuna matsayin Sin na babbar mai saye da sayarwa. Yanzu haka, yanayin duniya na cike da sarkakiya da sauye-sauye, kuma tubalin ingantuwar tattalin arzikin Sin yana bukatar karin karfi. Sai dai ya kamata a lura cewa, abubuwan dake ingiza ci gaba mai inganci a kasar na ci gaba da karuwa, lamarin da ke samar da goyon baya mai karfi ga burin kasar na samun karuwar tattalin arzikinta. (Fa’iza Mustapha)



















