Shugaba Xi Ya Taya Jamiar Hunan Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya tsangayu, da dalibai, da tsoffin daliban jamiar Hunan murnar cikar jamiar shekaru 100 da kafuwa. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar, ya gabatar da sakon taya murnar ne ta cikin wata wasika da ya aiki ga jamiar. Xi, ya kuma yi kira ga jamiar da ta ci gaba da aiwatar da akidunta na samar da sauye-sauye, da daga matsayi da ingancin koyarwa, kana ta matse kaimi wajen kyankyashe karin masu hazaka, wadanda ka iya amfani da abubuwan da suka koya a harkokin rayuwa na hakika, ta yadda hakan zai samar da sabbin gudunmawa ga aikin gina kasar Sin, har ta kai ga zama babbar cibiyar ilimi, da ingiza salon zamanantarwa irin na Sin. An kafa jamiar Hunan ne a shekara 1926, ta kuma cimma nasarar yaye tarin dalibai masu hazaka a tsawon wannan karni. (Saminu Alhassan)



















