Xi Ya Kai Ziyara Birnin Ulanqab Dake Jihar Mongoliya Ta Gida
Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja, Xi Jinping, ya jaddada cewa ci gaba mai kiyaye muhalli, muhimmin bangare ne na ci gaba mai inganci. Ya yi kira da a daidaita ci gaba mai inganci tare da kare muhalli, da tsayawa tsayin daka kan kiyayewa da kula da tsaunuka, da ruwa, dazuzzuka, gonaki, tafkuna, ciyayi, da hamada baki daya. Ya ce ya kamata a dage wajen samar da tsarin da ya dace don rage fitar da sinadarin carbon, da dakile gurbacewar muhalli, da fadada korayen wurare, da kuma bunkasa ci gaban tattalin arziki, yayin da ake ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen bin hanyar ba da fifiko ga kiyaye muhalli. Xi ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarci birnin Ulanqab dake jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta yau 16 ga wata. Bayan binciken yanayin kiyaye muhalli da kuma ci gaban masana’antu masu kiyaye muhalli a Ulanqab, Xi Jinping ya jaddada cewa kasar Sin kasa ce mai girma wadda ke da bambance-bambancen yankuna a fannin albarkatun kasa. Ya ce ya kamata kowane yanki ya dogara da ci gabansa bisa yanayinsa, ya yi amfani da fa’idodin da yake da su, sannan ya inganta ci gaba mai inganci ta hanyar da ta dace da yanayin yankinsa. (Safiyah Ma)



















