Reshen Jihar Kebbi na Jam’iyyar ADC ya bayyana shari’ar da Hukumar EFCC ke yi wa dan takararta na gwamna kuma tsohon Ministan Shari’a na Kasa, Abubakar Malami (SAN), a matsayin bita-da-kulli na siyasa. Jam’iyyar ta jaddada cewa wannan kalubale na shari’a ba zai taba kawo cikas ga aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027 ba.
Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da Shugaban Jam’iyyar na Jiha, Engr. Sufiyanu Bala, da kuma Shugaban Dattijai na ADC, Alhaji Shehu Aliyu Sambawa, suka sanya wa hannu a birnin Abuja. Sun yi zargin cewa ana amfani da shari’ar ne domin tsoratar da ‘yan adawa gabanin zabukan 2027.
Zargin Kokarin Musgunawa ‘Yan Adawa
Duk da cewa jam’iyyar ta bayyana goyon bayanta ga duk wani bincike ko shari’a ta halal ga wanda aka kama da laifi, ta nuna cewa lamarin Malami yana dauke da alamun gallazawa ta siyasa da nufin raunana ‘yan adawa a Jihar Kebbi.
Abubakar Malami, wanda ya rike mukamin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, a yanzu haka yana neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kebbi a karkashin inuwar jam’iyyar ADC. Jam’iyyar ta jaddada cewa babu wani “shari’ar kafafen yada labarai” ko tsoratarwa da zai hana su cimma nasara a 2027.














