Wani sakamakon binciken ra’ayin jama’a da cibiyar bincike ta Pew ta fitar a watan Yuli ya bayyana cewa, mutanen kasashe da yankuna 27 daga cikin 36 da aka yi binciken, sun fi nuna amincewa da Sin fiye da Amurka. Wannan shi ne karon farko da aka samu irin wannan sakamako bisa binciken Pew cikin kimanin tsawon shekaru 20. Ko a tsakanin kasashen kawancen Amurka ma, mutanen Burtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da sauransu sun fi nuna amincewa da Sin fiye da Amurka.Cibiyar bincike ta Pew ta gudanar da binciken daga ranar 8 ga watan Fabrairu zuwa 13 ga watan Mayu, inda ta ji ra’ayoyin mutane baligai 42,151 daga kasashe 36.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin kasashe 17 masu matsakaicin kudin shiga, kashi 75% na masu bayyana ra’ayoyi suna ganin cewa, Amurka tana “tsoma baki cikin harkokin gida na wasu kasashe”, yayin da kashi 45% kawai ke ganin Sin a matsayin hakan. Yawancin masu bayyana ra’ayin sun bayyana Sin a matsayin “sahihiyar abokiyar hadin gwiwa mai aminci”, wadda ta taka rawar gani ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.Bari mu duba dalilan da suka haifar da wannan bambanci.
Na farko, yakin Iran na kara tsananta saboda Amurka ta shiga dumu-dumu, kuma kasar Amurka ta kara harajin fito kan yawancin kasashen duniya, kana ta yi barazanar mamaye Greenland da Kanada, har ta rage taimakon da take bayarwa ga kasashen waje sosai, dukkan matakan suna kara bayyana matsayinta na shiga sharo ba shanu.
A daya hannun kuwa, tsarin hadin gwiwar Sin kamar “shawarar ziri daya da hanya daya” da “dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka” ya samar wa mabambantan kasashe kyakkyawar makomar hadin gwiwa.Ba wai daga manyan manufofi kawai aka samu gyaran fahimtar ainihin kasar Sin ba, har ma ana iya ganin dalilai daga rayuwar yau da kullum. A shafukan sada zumunta, “tafiye-tafiye a Sin” da “sayayya a Sin” suna kara habaka da samun karbuwa.
Karin masu yawon bude ido daga kasa da kasa suna zuwa Sin, inda suke gane wa idanunsu yadda Sin ke kasancewa mai tsaro da kuzari da kaunar baki.
Ban da haka, kayayyakin kamfanonin Sin kamar Huawei da BYD da ANTA da sauransu sun riga sun shiga cikin rayuwar mutanen duniya.Masaniyar bincike na Pew, Laura Silver, ta nuna cewa, mutanen duniya sun jefa kuri’u ne bisa gaskiyar da suka gani, matakin da ya haifar da wannan canji da ba a taba gani a binciken Pew ba a tarihi.Kamar yadda jaridar People’s Daily ta bayyana a cikin sharhinta, “Dalilin da ya sa Sin ta sami wadannan nasarorin shi ne, ta nace ga bin hanyar zamanantarwa mai salon kanta.
Wannan hanyar, ba wai kawai ta dace da yanayin Sin ba, har ma ta bai wa kasashen duniya sabon zabi na zamanantar da kansu.” Wato lokacin da karin kasashe suka gani da ido nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen zamanantar da kansu, ba kawai suka gyara fahimtar kasar Sin ba, har ma da wata sabuwar hanyar samun ci gaba.
Wane ne ke haifar da rikici, kuma wane ne ke samar da damammaki? Wane ne ke kafa shingaye, kuma wane ne ke gina gadar ci gaba? Wane ne ke keta hakkin jama’a, kuma wane ne ke sanya muradun jama’a a gaban kome? Kowa ya gani da ido yadda Sin ke himmatuwa wajen bunkasa kanta da kuma amfanar da duniya baki daya. (Marubuciya: MINA)














