An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal
An karrama masana ilimin lissafi na kasar Sin da suka hada da Deng Yu da Wang Hong da lambobin yabo...
An karrama masana ilimin lissafi na kasar Sin da suka hada da Deng Yu da Wang Hong da lambobin yabo...
Duk da gargadin da bangaren Sin ya maimaita sau da dama, jiragen ruwan gwamnatin Philippines guda biyu sun kutsa kai...
An kira taron ministocin kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki ta nahiyar Asiya da tekun Pasific (APEC), kan harkar raya fasahohin dijital da kirkirarriyar basira ko AI na shekarar 2026, jiya Alhamis a birnin Chengdu na kasar Sin, inda aka zartas da sanarwar ministocin kungiyar APEC na shekarar 2026 game da ayyukan raya fasahohin dijital da AI, ko kuma sanarwar Chengdu a takaice. Cikin sanarwar, an cimma matsaya daya ta kafa kungiyar hadin gwiwar raya fasahohin digital da AI ta yankin Asiya da Pasifik, domin kafa tsarin zurfafa hadin gwiwa a fannin raya fasahohin tsakanin mambobin kungiyar APEC a nan gaba. Shugaban taron, kana ministan harkokin masana’antu da sadarwa na kasar Sin Li Lecheng ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da mambobin kungiyar ta APEC, ta hanyar amfani da tsarin kungiyar, da aiwatar da ra’ayi daya da aka cimma yayin taron na wannan karo, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakanin bangarori daban daban, don cimma moriyar bunkasuwar fasahohin dijital da AI, da kafa makoma mai haske cikin hadin gwiwa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
A yau Jumma’a, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da matakin sanya kamfanoni 14 na Tarayyar Turai (EU) cikin...
Lamarin gibi ta fuskar ci gaba tsakanin gabashin da yammacin Sin wani batu ne da ake yawan tattauna a kansa...
Ma’aikatar aikin gona da kula da harkokin yankunan karkara ta kasar Sin ta sanar a yau Jumma’a cewa, yawan hatsin da kasar ta girbe da lokacin zafin bana ya kai wani sabon matsayi na tan miliyan 150.75, inda ya zarce adadin tan miliyan 150 a karon farko. Mataimakin ministan aikin gona da kula da harkokin yankunan karkara, Zhang Xingwang, ya fada wa wani taron manema labarai cewa, ya zuwa yanzu kasar ta samar da jimillar filayen noma masu inganci da suka haura hekta miliyan 66.7, lamarin da ya ba da damar girbe amfanin gona mai yawa da ke samun karuwa a jere. A rabin farko na shekarar, kasar Sin ta kuma kara kaimi wajen bunkasa masana’antarta ta samar da iri. A halin yanzu dai, nau’o’in amfanin gona da aka samar a cikin gida sun kai fiye da kashi 95% na jimillar wadanda aka shuka a filayen noma. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Wani bincike kan ra'ayoyin jama'a da cibiyar bincike ta Pew ta kasar Amurka ta gudanar kwanan nan ya nuna cewa,...
A watan Yulin shekara ta 2026, a birnin Shanghai. A wurin taron raya kirkirarriyar basira ko AI na duniya, mahalarta...
Kasar Sin ta ci gaba da kasancewa wuri mai jan hankulan masu zuba jari daga kasashen waje, inda kamfanoni kusan 4,800 masu jarin waje suka kara yawan jarin da suke zubawa a kasar a rabin farko na shekarar 2026, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar a yau Alhamis. A cikin watanni shida na farko na shekarar, kasar Sin ta samu karuwar kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje da kashi 5.3% a mizanin shekara-shekara, inda jarin waje da ake zubawa kai-tsaye (FDI) wanda ake amfani da shi a zahiri ya kai yuan biliyan 402.1, watau kwatankwacin dala biliyan 59.2. Tsarin zuba jarin waje ya ci gaba da samun bunkasa, inda jarin da aka zuba a masana’antun manyan fasahohin zamani ya karu da kashi 33.2% a mizanin shekara-shekara, wanda ya kai kashi 42.4% na daukacin jimillar da aka zuba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau Alhamis, domin yin bayani a kan ayyukan kasuwanci da yadda aka tafiyar da su a rabin farkon shekarar 2026. Shugabar sashen kula da jarin waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar, Meng Huating ta mayar da amsa ga tambayoyin da suka shafi harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, inda ta bayyana cewa, a halin yanzu, tawagogin kasuwanci na bangarorin biyu suna tuntubar juna game da tsarin kwamitin cinikayya, ayyukansa, da kuma yadda za a gudanar da shi, kana suna tattaunawa kan yadda za su ciyar da shirin rage harajin fito na yi-min-na-rama na dala biliyan 30 ga kowane bangare gaba. Jami’ar ta kuma kara da cewa, bangaren Sin yana sauraron ra'ayoyin masu ruwa da tsaki daban-daban, ciki har da kamfanoni da kungiyoyin kasuwanci na cikin gida, da kananan hukumomin kasar, da kuma kungiyoyin kasuwanci na kamfanonin jarin Amurka da dai sauransu, game da shawarwarin tsarin rage haraji. Shi bangaren Amurka kuma yana neman ra'ayoyin jama'a game da kwamitin cinikayya da kuma ayyukan rage harajin fito. A cewar jami’ar, bangarorin biyu za su ci gaba da tuntubar juna ta kut-da-kut, da gaggauta cimma matsaya kan tsarin rage haraji ga takamaiman kayayyaki tare da inganta aiwatar da shi, da nufin kara fadada cinikayyar da ke tsakaninsu. (Bilkisu Xin)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.