ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Sin

A watan Yulin shekara ta 2026, a birnin Shanghai. A wurin taron raya kirkirarriyar basira ko AI na duniya, mahalarta taron sama da 1,400 sun shaida kafuwar kungiyar hadin gwiwar AI ta duniya WAICO a hukumance, wadda ta zama irinta na farko a duniya. Duk a wajen taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping a jawabinsa ya sanar da cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta ba da horo na musamman kan fasahar AI ga mutane 5,000 daga kasashe masu tasowa, za ta kuma gina cibiyoyin hadin gwiwar ayyukan AI na duniya ga kungyiyoyin ASEAN, da AU da kasashen BRICS, da kuma inganta amfani da tsarin yin gargadin bala’un yanayi mai hikima da ake kira “Mazu” a kasashe 30.

Duk wadannan abubuwa sun bayyana matsayin da Sin take dauka kan fasahar AI, wato dole ne AI ta zama abu mai amfanin dukkan bil’adama, kuma raba fasahohi da hadin gwiwa da sanya muradun jama’a a gaban komai sun zama muhimman ka’idojin raya fasahar AI na duniya. Sin tana kokarin raba fa’idodin fasaharta tare da kasashe masu tasowa, don more damammaki a maimakon babakere.Amma a nasu bangare, kasashen yamma musamman ma kasar Amurka, sun bi wata hanya ta daban. Wani shehun malami dan Australiya, kuma mai ba da shawara ga tsohon firaministan Australia Kevin Rudd kan harkokin manufofi, Warren Rodwell, ya wallafa wani sharhi kwanan nan yana mai cewa, wasu ’yan kamfanonin kasashen yamma kamar su Open AI da Google da Nvidia su kan kwashe bayanai kyauta daga wasu kasashe masu tasowa bisa tsarin da suka tsara da kan su da babakerensu a fannin samun bayanai, daga baya su sayar wa kasashe masu tasowa hidimomin AI bisa farashi mai tsada.

Kana, kalaman wani malami mai ziyara a jami’ar ACU ta Ghana, Emmanuel Gadasu, sun kara tabbatar da babakeren da kasashen yamma ke yi wa kasashe masu tasowa a bangaren dijital. Ya nuna cewa, kasashe masu tasowa sun ba da gudunmawa mai yawa na tattara bayanan horo don tabbatar da ci gaban fasahar AI, amma ba su sami daidaitaccen kudin shiga ko fasaha bisa ayyukan da suka yi ba, kuma an kwashe bayanansu kyauta, matakin da ya kara fadada gibin ci gaban dijital tsakanin kasashe masu wadata da kasashe masu tasowa.

ADVERTISEMENT

A hannu guda kuwa, Sin ta bi wata hanya ta daban. Farashin bincike da amfani da samfuran fasahar AI na kasar Sin kamar DeepSeek ya kai kashi 5 zuwa 10 cikin 100 bisa na kasashen yamma. Wannan tsarin hadin gwiwar AI na bude kofa mai rahusa kuma mai saukin amfani ya ba da dama ga kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, da su ci gajiyar fa’idodin damammakin fasahar Sin cikin sauri, alal misali yawan saukar da manyan samfuran AI da Sin ta samar ba tare da shingaye ba a duniya ya wuce sau biliyan 10, wanda ya taimaka wa kasashe masu tasowa su yi amfani da sabbin fasahohi da kayayyaki.

A Kigali, babban birnin Rwanda, masu kirkire-kirkire na fasahar hada-hadar kudi sun fara amfani da tsarin AI na kyauta irin na Sin don horar da samfuran AI na gida. Sa’an nan a birnin Legas na Najeriya, sabbin kamfanonin fasahar noma suna amfani da nau’ikan samfuran AI na kyauta don kirkirar kayan aikin gano cututtukan abubuwan da aka shuka irinsa rogo. Ban da haka, a jami’ar Zimbabwe, cibiyar manyan kwamfutoci na mataki na biyu da Sin ta taimaka wajen ginawa ta fara aiki, kuma karfin lissafinta yana kan gaba a nahiyar Afirka. Tabbas, kasashen Afirka za su iya dogaro da fasahar Sin ta kyauta don bunkasa karfinsu na kirkire-kirkire.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Bambancin tsare-tsaren biyu, ya wuce maganar fasaha. A hannu guda, kwararru dake Silicon Valley na kasar Amurka suna kallon AI a matsayin “kayan aikin wayewar kai”, suna gina shingaye bisa tsarin fasaharsu, da mallake fasaha; a hannu guda kuma, Sin ta mai da fasahar AI a matsayin mai samar da fa’ida ga dukkan bil’adama, tare da samar da fasahohi kyauta, ta yadda fasaha za ta amfanar da talakawa a ko ina. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba bayyana cewa: ” Bai kamata ci gaban AI ya zama tamkar wasan kide-kide na wata kasa daya kadai ba, a’a, ya kamata ya zama wasan kide-kide na hadin gwiwar duniya.” Tabbas ne, hanyar hadin gwiwa ta samar da fasahohi kyauta ta Sin za ta kai ga samar da makoma mai adalci ta dijital a duniya nan gaba.(Marubuciya: MINA)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.