An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu
A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin tattauna batutuwan zaman lafiya da tsaro na Sin da nahiyar Afirka karo na hudu a nan birnin Beijing. Taron ya gudana ne karkashin jigon "Gina tsaro tare: Shekaru 70 na goyon bayan juna, yin aiki kafada-da-kafada a sabon zamani", ya kuma hallara wakilai daga sassan hukumomin tsaro, da na soji, da jakadun da ke aiki a nan kasar Sin na kasashe membobin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da kasashen Afirka 41. Ministan ma’aikatar tsaron kasar Sin Dong Jun, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa Dong Jun, ya ce a bana ake bikin cika shekaru 70 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kuma hadin gwiwar tsaro tsakanin Sin da nahiyar Afirka ya haifar da ci gaban sassan biyu, da ma daidaiton yanayin kasa da kasa. Kazalika, ya ce kamata ya yi sassan biyu su aiwatar da matakan wanzar da kawancen gargajiya, da dagewa wajen bin turbar hadin gwiwa ta tsawon lokaci, wanda ke wakana bisa zaman daidai-wa-daida da cimma moriya tare. Ministan tsaron na Sin ya kara da cewa, rundunar sojojin kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da bangaren kasashen Afirka wajen karfafa tsare-tsare, da inganta tsarin musayar tsaro mai game dukkanin fannoni, kuma mai matakai daban daban, da zurfafa hadin gwiwar tsaron teku na shiyyoyi, da kyautata ikon wanzar da tsaro a sabbin fannoni, da samar da karin nasarori na hakika, ta yadda za a iya bayar da sabbin gudunmawa wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani daga dukkanin fannoni. A nasu bangaren, wakilan Afirka a taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ke takawa, a matsayinta na muhimmiyar kawa ga kasashen Afirka, suna masu bayyana yadda tsaron nahiyar ya hade cikin na sauran sassan duniya. Har ila yau, sun kuma bayyana aniyarsu ta kara karfafa hadin gwiwa da Sin a harkokin tsaro, kana da bayar da gudunmawa ga ci gaban alakar Afirka da Sin. (Saminu Alhassan)

















