Ga duk mai bibiyar irin ci gaban da kungiyar BRICS ke samu a shekarun baya bayan nan, ya kwana da sanin irin tasirinta ga dukkanin kasashe membobi 11, da abokan hulda 10, a fannin samar da kakkarfan ginshikin ci gaban bai daya.
A yayin taron kungiyar karo na 18 wanda ya gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya a baya bayan nan, a kuma gabar da kungiyar ke cika shekaru 20 da kulla alakar hadin gwiwa, mun ga yadda aka tattauna batutuwan zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai inganci, wanda zai dore ba tare da tangarda ba, da samar da sauye-sauye na inganta tsarin jagorancin duniya, da musayar al’adu, da kuma makomar tsarin tattalin arzikin duniya.
Idan mun waiwaiyi tarihi, za mu fahimta cewa kungiyar BRICS ta kafu ne a shekarar 2006 da kasashe membobi guda hudu, wato Brazil, da Rasha, da Indiya da Sin, kuma ya zuwa yanzu ta zamo wani rukuni mai karfin gaske na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da masu samun saurin ci gaba.
Hakan ya sa masu fashin baki ke ganin dacewar amfani da wannan dandamali na BRICS, wajen kara dinke tafiya tsakanin sassan kasashe masu tasowa da masu saurin samun ci gaba ta yadda za su yi aiki tare, domin ingiza daidaito, da kara karsashi da bunkasa walwalar dukkanin bil’adama.
Tun kafuwarta, tsarin hadin gwiwar BRICS na da alaka mai karfi da burin kasashe masu tasowa na bunkasa kasuwanninsu. A yanzu kuma, membobin kungiyar sun samu karfi, da kuzari na yayata muryar bai daya a batutuwan kasa da kasa, yayin da suke kara aiki tukuru tare da sauran kasashe masu tasowa wajen cimma moriyar bai daya.
Yayin da hadin gwiwar BRICS ke shiga sabon mataki na ci gaba, aiki dake gaban kungiyar na kara fitowa fili, wato aiwatar da matakai masu fadi da zurfi kuma masu nagarta.
BRICS ba kungiyar zaman shan shayi ba ce, domin kuwa ayyukanta sun tabbatar da matsaya ta fada-da-cikawa. Kungiya ce wadda ke kara bayyana kanta ta hanyar aiki na hakika, kuma ake iya ganin sakamakon ayyukanta a zahiri. Kasashe membobinta na asali irinsu kasar Sin, na ci gaba da ingiza sabon karfi na bunkasa hadin gwiwa, ta hanyar gabatar da shawarwari, da tsare-tsare na hakika da nufin cimma nasarorin bai daya.














