Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci ’yan Nijeriya da ke son sayen hannun jarin matatar man Dangote da ka da su yi amfani da kuɗin da suke buƙata domin muhimman abubuwan rayuwa.
Sanusi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron wayar da kan masu zuba hannun jari kan sayar da hannayen jarin matatar Dangote da aka gudanar a Kano.
Ya shawarci mutane da su zuba hannun jari ne da kuɗin da za su iya ajiyewa na tsawon lokaci, maimakon amfani da kuɗin makarantar ’ya’yansu ko sayar da gidajen da suke zaune.
“Ka da ku ɗauki kuɗin makarantar ’ya’yanku ku saka a hannun jari. Ka da ku sayar da gidan da kuke zaune ku saka kuɗin a hannun jari,” in ji Sarkin.
Ya ba da shawarar cewa mutane su fara da kuɗaɗe kaɗan kamar Naira 10,000, Naira 20,000 ko Naira 30,000, gwargwadon abin da za su iya warewa.
Sarkin ya kuma shawarci masu zuba hannun jari da ka da su sayi hannun jari da nufin samun riba cikin gaggawa.
Ya ce ya kamata su yi haƙuri kuɗin na tsawon lokaci domin ya samu damar ƙaruwa.
Ya bayyana cewa duk da matatar tana Legas, hakan ba zai hana masu sayen hannun jari samun ribarsu ba, domin kamfanin mallakin masu hannun jarin ne, kuma su ne ke da haƙƙin riba a kamfanin.
Sanusi ya kuma yaba wa Aliko Dangote, tare da ƙarfafa gwiwar al’ummar Kano su yi la’akari da mallakar hannun jari a kamfanin kafin lokacin sayar da hannun jarin ya ƙare.













