Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, sun yi kira da a ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu bayan shekarar 2027.
Sun bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taron tsoffin shugabannin majalisun dokokin jihohi, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Lalong ya buƙaci ’yan Nijeriya su goyi bayan Tinubu domin ya sake zama shugaban ƙasa a karo na biyu, yana mai cewa gwamnati na buƙatar ƙarin lokaci domin kammala shirinta na sauye-sauyen tattalin arziƙi.
Ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mataki mai wahala wanda ya zama dole, yana mai cewa hakan zai bai wa gwamnati damar karkatar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafi zuwa fannoni kamar noma, masana’antu, ababen more rayuwa, ilimi, makamashi da fasaha.
Lalong ya ce Tinubu ya yi namijin ƙoƙari wajen ɗaukar matakan da gwamnatocin baya suka kasa ɗauka, yana mai cewa ya kamata a ba shi damar kammala ayyukan da ya fara.
Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da su riƙa bayyana wa ’yan Nujeriya dalilan da suka sa aka kawo sauye-sauyen, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka samu sakamakon matakan ana amfani da su yadda ya kamata wajen bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.
A cewarsa, Nijeriya na buƙatar sauya tsarin dogaro da amfani da kayan gwamnati zuwa hanyoyin saka hannun jari.
Ita ma Uwargidan Shugaban Ƙasa ta yi kira da a kare nasarorin da gwamnatin ta samu domin amfanin ’yan Nijeriya na yanzu da kuma na nan gaba.
Ta yaba da goyon bayan da mahalarta taron suka nuna wa Tinubu domin ya sake tsayawa takara a karo na biyu, tana mai cewa hakan na da muhimmanci saboda ya fito daga tsoffin shugabannin majalisun jihohi da suka san ƙalubalen shugabanci da ɗaukar manyan matakan gwamnati.
Uwargidan Tinubu ta kuma buƙaci tsoffin ’yan majalisa da su ci gaba da bai wa ƙasa gudummawa, saboda ƙwarewarsu na iya taimakawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da koyar da matasa shugabanci.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Jagoranci Na Gari, Sauye-Sauye: Daga Tallafi zuwa Sabon Muradi.”














