Gwamnatin yankin musammam na Hong Kong na kasar Sin, ta fitar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewa na shekaru 5, a jiya Laraba. Wannan shi ne karo na farko da aka fitar da cikakken shiri domin raya tattalin arziki da zamantakewa a yankin na musammam na Hong Kong.
Shirin na shekaru 5 ya alamta shigar yankin cikin fagen shugabancin al’umma mai mayar da hankali kan cikakken tsari mai hangen nesa da fada da cikawa. A matsayinsa na wurin da aka fi gudanar da harkokin tattalin arziki cikin ‘yancin a duniya, kuma cibiyar hada-hadar kudi ta duniya, Hong Kong ya zama wata muhimmiyar kasuwa mai tasiri a yankin kudu maso gabashin Asia da yammacin Asia da kudancin Amurka a shekarun baya-bayan nan. Jerin harkokin da suka shafi hada-hadar kudi da cinikayya da matakan kirkire-kirkire da aka zayyana cikin shirin na shekaru biyar-biyar na farko, zai kara karfafa matsayin Hong Kong na cibiyar hulda da hada-hada.
Ana sa ran karkashin jagorancin shirin na shekaru biyar-biyar na farko, Hong Kong zai ci gaba da amfani da fifiko na musammam da yake da su na dogaro da babban yankin Sin da hadewa da sassan duniya, domin hawa sabon tafarkin shugabanci da samun wadata. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














