An Kaddamar Da Wani Kwas Na Horar Da Kwararru Kan Killace Kananan Makamai Na Sin Da MDD Da Afirka
A yau Talata ne aka gudanar da bikin kaddamar da ajin horar da kwararru, kan killace kananan makamai na Sin, da MDD da kasashen nahiyar Afirka a nan birnin Beijing, horon da Sin da MDD suka yi hadin gwiwar daukar nauyin gudanarwa, ga kasashen yankin manyan tafkunan Afirka ko “Great Lakes”. Horon ya samu halartar wakilai fiye da 20, daga kasashe 5 na yankin da suka hada da na Tanzania, da Uganda, da Burundi, da Congo Kinshasa, da Ruwanda, da jami’ai daga kungiyar AU, da kungiyar tarurukan kasa da kasa ta yankin, inda za su yi bita da tattaunawa tare, kan batutuwan killace kananan makamai a cikin gida, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Mataimaki ga ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Bin, ya bayyana a gun bikin kaddamarwar, cewa kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afirka, wajen sa kaimi ga ayyukan killace kananan makamai a yankin, da kaddamar da hadin gwiwa a wannan fanni a tsakanin bangarori daban daban da sassan kasa da kasa, da yankin baki daya, don inganta karfin kiyaye tsaron kasashen Afirka, da neman cimma burin kawar da harbe-harben bindiga a nahiyar Afirka, da kuma neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Zainab Zhang)



















