Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana binciken hotunan da ake zargin an ƙirƙira ta hanyar fasahar basirar ɗan’adam (AI) da suka bayyana a rajistar masu zaɓe ta farko, tare da gyara bayanan da aka gano suna da kura-kurai.
Hukumar ta bayyana cewa rajistar da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar 26 ga Oktoba, 2026, ita ce wadda aka nuna wa jama’a a faɗin ƙasar daga 9 zuwa 15 ga Oktoba. Ta ce wallafar ba ta ƙunshi dukkan gyare-gyaren bayanan da ake gudanarwa ba.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe na INEC, Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar ta gano wasu bayanan rajista da ake buƙatar bincika tun lokacin da aka nuna rajistar ga jama’a.
Ya ƙara da cewa hukumar tana binciken yadda hotunan da ake zargi suka shiga rajistar, ciki har da yiwuwar samun matsala ta fasaha ko kuma kura-kurai a tsarin gudanarwa. INEC ta ce za ta ɗauki matakin da ya dace bayan tabbatar da gaskiyar lamarin.
Hukumar ta jaddada cewa rajistar da aka wallafa ba ita ce ta ƙarshe ba. Za ta kammala tantancewa da gyaran bayanai kafin tabbatar da rajistar ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026.
INEC ta kuma yaba wa ’yan ƙasa da suka jawo hankalinta kan lamarin, tana mai cewa sa ido daga jama’a na taimakawa wajen inganta sahihanci da ingancin rajistar masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.














