Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya ce zai yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfen a zaɓen 2027 idan gwamnatinsa ta magance matsalar rashin tsaro tare da dawo da zaman lafiya a Sakkwato da sauran sassan Arewacin Nijeriya.
Bafarawa ya bayyana hakan ne a wata hira da kafar yaɗa labarai ta FRI, inda ya ce babban abin da yake so shi ne a bai wa jama’a damar komawa harkokinsu na yau da kullum, ciki har da zuwa makaranta, noma da gudanar da kasuwanci ba tare da fargaba ba.
Ya ce ba ya neman kuɗin kamfen ko wata alfarma daga Tinubu, sai dai matakan da za su tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.
A cewarsa, shugaban ƙasa na da isasshen iko, kuɗi da jami’an tsaro da za su iya taimakawa wajen sauya yanayin tsaro cikin wata ɗaya zuwa uku idan aka ba lamarin fifiko.
Bafarawa, wanda ya ce ba ya cikin jam’iyyar APC mai mulki, ya jaddada cewa zai goyi bayan duk wanda ya samar da zaman lafiya a Arewa, ciki har da Tinubu.
Ya kuma kare naɗin tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, a matsayin Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu, yana mai cewa Yari a matsayinsa na ɗan APC ya kamata ya mutunta matsayar jam’iyyarsa da buƙatar shugaban ƙasa.













