Ministan kula da harkokin wajen Burundi Edouard Bizimana, ya ce tafarkin Sin na samun ci gaba bisa dogaro da karfinta, ya zama mai karfafa wa sauran kasashe gwiwa, musamman kasashe masu tasowa.
Edouard Bizimana ya bayyana haka ne da yammacin ranar Laraba, yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. Bikin ya hada al’ummar Sinawa mazauna Burundi da jami’an gwamnatin kasar da kuma jami’an diplomasiyya da ke aiki a kasar.
A cewar ministan, salon ci gaban kasar Sin misali ne na dogaro da karfinta, kuma ya kamata ya karfafa wa sauran kasashe gwiwa, musammam kasashe masu tasowa, ciki har da Burundi.
Ya kuma bayyana fatan habakar dangantakar cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu, yana mai karfafa wa bangarori masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki, gwiwar amfani da damarmakin da dangantakar kasashen biyu ta samar. (Fa’iza Mustapha)














