ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

by Sadiq
1 hour ago

Wani matashi da ya tsira daga inda sama da matasa 30 da suka rasu waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Neja, ya yi zargin cewa an fesa wani sinadari a ɗakin da aka tsare su, kafin wasu daga cikinsu su fara faɗuwa.

Matashin da ya tsira ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin ziyarar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kai jihar.

Ziyarar ta biyo bayan mutuwar mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke hannun Hukumar Tsaron ta NSCDC.

ADVERTISEMENT

A cewar matashin, an fesa wani abu a cikin ɗakin jim kaɗan shigar da su, sannan wasu daga cikinsu suka fara faɗuwa.

An kama waɗanda ake zargin ne yayin wani samame da aka gudanar kan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Wushishi/Lukoto na Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga watan Satumba.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

Har yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar matasan ba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.

Tun da farko, Ministan Harkokin Cikin Gida ya dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, tare da ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Hukumar NSCDC ma ta kafa kwamitin bincike domin duba halin da waɗanda aka tsare suke ciki lokacin da aka kama su, yadda aka kula da su yayin da suke tsare.

Ana sa ran binciken zai gano abin da ya faru kafin mutuwar matasan.

MASU ALAKA

Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 18, 2026
Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna
Manyan Labarai

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

September 18, 2026
Ka Da Ku Siyar Da Gidajenku Don Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote – Sanusi II
Manyan Labarai

Ka Da Ku Siyar Da Gidajenku Don Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote – Sanusi II

September 17, 2026

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

September 18, 2026
Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

September 18, 2026
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 18, 2026
Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

September 18, 2026
ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

September 18, 2026
Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

September 18, 2026
Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

September 18, 2026
Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

September 18, 2026
Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

September 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.