Kwamitin kare hakkin dan adam na MDD na gudanar da taro na 63 a Geneva. Kwanan nan, wakilin Sin ya yi kira a yayin taron da a kara mai da hankali a fannin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu. Wannan kira ya shafi ainihin bukatun kasashen Afirka, abin da al’ummar Afirka ke mai da hankali a gaban kome shi ne, ko za a iya fita daga talauci, ko za a iya samun ci gaba, ko za a iya wadata, har ma ko za a iya rayuwa? A ganinsu, hakkin dan adam ba wata alama ta siyasa ba ce kawai.
Kwamitin kare hakkin dan adam yana da tsare-tsare guda 13 na musamman mai bincike kan kasa da kasa, dukkansu suna mai da muhimmanci kan kasashe masu tasowa, suna kashe miliyoyin daloli, amma ba su mayar da hankali sosai kan matsalolin hakkin dan adam da suke fi bukatar kulawa ba. Yayin da ’yan siyasar kasashen yamma ke yada jita-jita da labaran karya da nuna fuska ta biyu, a wani bangare kuwa yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kango na fuskantar bala’in jin kai sakamakon rikicin makamai, kuma sama da mutane miliyan 30 a Sudan na bukatar taimakon jin kai. Wasu kasashe suna sha’awar mayar da kwamitin kare hakkin dan adam fagen takara a bangare siyasa, yayin da kasashe masu tasowa da dama, musamman kasashen Afirka, ke fuskantar karancin ci gaba da matsalolin rayuwar al’umma, amma ana barin su a gefe.
A daya bangaren kuma, ayyukan Sin wajen tabbatar da hakkin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu na da amfani mai ma’ana ga Afirka. Sin ta kammala aikin kawar da talauci a kan lokaci, mutane miliyan 98.99 na karkara dake cikin talauci duk sun fito daga kangin talauci, kuma gundumomi 832 masu fama da talauci ma dukkansu sun kawar da kangin talauci. Sama da mutane biliyan 1.3 a Sin suna cikin tsarin inshorar lafiya mai tushe, kuma adadin masu shiga ya tsaya tsayin daka sama da kashi 95%. Nasarorin da Sin ke samu wajen kare hakkin dan adam marawa Sin bayan wajen shiga harkokin kula da hakkin dan adam na duniya, kuma irin wannan dabara abin da Afirka ta fi bukata ke nan.
Hadin gwiwar Sin da Afirka na ci gaba da bin ka’idar “Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni” don taimakawa Afirka ta kara bunkasa ci gaban kanta, kuma wannan shi ne mataki mafi amfani wajen tabbatar da hakkin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu.
A fannin tabbatar da isashen abinci, Sin na yada fasahar shinkafa mai sauri a kasashen Zimbabwe da Chadi. A lardin Mashonaland ta Yamma na Zimbabwe, kwararrun Sin sun kafa “gidan renon kaji”. A kauyen Medken na Chadi, gonar misali ta samar da shinkafa ton 10.03 a kowace hekta, wanda ya kai kusan ninki 3 na matsakaicin yawan amfanin gona na yankin.
A fannin kiwo lafiya kuwa, cikin fiye da shekaru 60 da suka gabata, tawagar likitocin Sin dake taimakawa Afirka sun tura kusan ma’aikata 26,000 zuwa kasashen Afirka 48, suna jinyar marasa lafiya miliyan 230. A shekarar 2026, lokacin da annobar Ebola ta barke a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kango, Sin ta tura tawagogin kwararrun likitocin yaki da annobar sau 3 a jere.
A yayin taro na 63 na kwamitin kare hakkin dan adam, wakilin Sin ya yi kira da a kara mai da hankali a fannin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu. Wannan shi ne abin da Sin ke yi a cikin gida da kuma a nahiyar Afirka. Yayin da wasu kasashe ke daukar hakkin dan adam a matsayin makamin siyasa na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe, Sin tana kokarin tura kayan aikin noma na zamani, iri da magunguna da fasaha zuwa kasashen Afirka, don taimaka musu wajen kawar da talauci da samun ci gaba da wadata. Wane ya dauki ainihin matakan tabbatar da hakkin dan adam? Al’ummar Afirka za su iya ganewa idanunsu da kansu. (Marubuciya: MINA)














