ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

by Sulaiman
52 minutes ago
Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai na yau da kullum da ya gudana yau Jumma’a cewa, Sin ta bukaci Japan ta fuskanci tarihinta na mamayar zalunci tare da yin waiwaye mai zurfi a kai, sannan ta yi kokarin samun yardar makwabtanta na Asiya da kuma kasashen duniya baki daya ta hanyar daukar kwararan matakai na zahiri.

Guo ya bayyana cewa, musanta laifin mamayar zalunci na nufin kalubalantar abubuwan da aka kammala tabbatarwa a tarihi da kuma kawo cikas ga tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu, inda ya jaddada cewa, dole ne dukkan kasashen yankin, ciki har da kasar Sin, su kasance cikin matukar taka-tsantsan, tare da hana sake ganin tara karfin soji na Japan da kuma hana sake barin masifun da suka faru a tarihi su maimaita kansu.

A yau Jumma’a, an kunna jiniya da kada kararrawa a yankin arewa maso gabashin kasar Sin domin cika shekaru 95 da faruwar al’amarin ranar 18 ga watan Satumba, wanda ya zama farkon yakin turjiyar kasar Sin ga mamayar zaluncin kasar Japan.

ADVERTISEMENT

A ranar 18 ga watan Satumbar 1931 ne dai sojojin Japan suka tarwatsa wani bangare na layin dogo da ke karkashin ikonsu a kusa da birnin Shenyang, inda suka zargi sojojin kasar Sin da yin zagon kasa don kawai su samu hujjar harin da suka kai sansanin soji da ke kusa da Shenyang a ranar da dare, tare da kaddamar da mamayar da suka shirya munakisarta tun farko a kan kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana
  • Sulaiman
    Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan
  • Sulaiman
    Samun Ci Gaba Shi Ne Abu Mai Tushe Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana
Daga Birnin Sin

September 18, 2026
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali
Daga Birnin Sin

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

September 18, 2026
Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

September 18, 2026

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

September 18, 2026
Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026
Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

September 18, 2026
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

September 18, 2026
‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

September 18, 2026
Samun Ci Gaba Shi Ne Abu Mai Tushe Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam

Samun Ci Gaba Shi Ne Abu Mai Tushe Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam

September 18, 2026
Gwamnatin Najeriya Na Daukar Darasi Daga Salon Da Kasar Sin Ke Amfani Da Shi Na Kulla Alakar Diflomasiyya Ta Hanyar Jan Hankali Da Kyakkyawar Mu’amala

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

Babban Jami’in Kasar Burundi: Ci Gaban Kasar Sin Abu Ne Mai Karfafa Wa Sauran Kasashe Gwiwa

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci