Bisa kididdigar da hukumar aike da sakwanni ta kasar Sin ta bayar, an ce, sana’ar aike da sakwanni a Sin, ta ci gaba da bunkasa cikin kwanciyar hankali daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana. Masana’antar na mai da hankali kan bukatun kasuwa na jigilar kayan gwari da kayayyakin gona da abincin teku na musamman, kuma tana ci gaba da inganta ayyukan jigilar kayayyaki.
Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana, jimillar ayyukan jigilar kayayyaki ta kai biliyan 145.46, wadda ta karu da kashi 4.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma kudaden shiga a wannan bangare (ba tare da kudaden shiga dake shafar kudin ajiya a bankin tura sakonni na Postal Savings ba) ya kai Yuan triliyan 1.23045, wanda ya karu da kashi 6.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma sana’ar gaba daya na ci gaba da habaka cikin kwanciyar hankali. (Amina Xu)
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar HankaliBisa kididdigar da hukumar aike da sakwanni ta kasar Sin ta bayar, an ce, sana’ar aike da sakwanni a Sin, ta ci gaba da bunkasa cikin kwanciyar hankali daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana. Masana’antar na mai da hankali kan bukatun kasuwa na jigilar kayan gwari da kayayyakin gona da abincin teku na musamman, kuma tana ci gaba da inganta ayyukan jigilar kayayyaki.Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana, jimillar ayyukan jigilar kayayyaki ta kai biliyan 145.46, wadda ta karu da kashi 4.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma kudaden shiga a wannan bangare (ba tare da kudaden shiga dake shafar kudin ajiya a bankin tura sakonni na Postal Savings ba) ya kai Yuan triliyan 1.23045, wanda ya karu da kashi 6.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma sana’ar gaba daya na ci gaba da habaka cikin kwanciyar hankali. (Amina Xu)














