Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen magance matsalar yunwa da rashin isasshen abinci mai gina jiki ga yara, ta hanyar kafa rumbunan abinci na al’umma da kuma faɗaɗa shirin rabon kayan abinci ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI).
Oluremi ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Akure, babban birnin Jihar Ondo, yayin rabon kayan abinci ga rukunin masu buƙata na musamman a jihar.
Uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, wadda ta wakilce ta a wajen taron, ta ce wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙudurin Renewed Hope Initiative na tallafa wa ‘yan Nijeriya masu rauni tare da tabbatar da cewa yara sun samu damar girma cikin ƙoshin lafiya da walwala.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce shirin Renewed Hope Initiative na taimaka wa aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta hanyar ba ‘yan Nijeriya damar cimma burinsu ba tare da la’akari da halin rayuwarsu ko matsayinsu ba, tare da magance matsalar ƙarancin abinci da rashin isasshen abinci mai gina jiki.
Ta bayyana cewa an ƙaddamar da Shirin Raba Kayan Abinci ne a watan Maris na shekarar 2024 domin samar da kayan abinci ga masu nakasa da sauran rukunin al’umma masu buƙata, tare da tallafa wa iyalansu da inganta rayuwarsu.
Ta ce, “Ba ma son wani ɗan Nijeriya ya kwana da yunwa. Wannan shi ne nauyin da ke kanmu kuma yana daga cikin manufofinmu a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative.”













