ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Shirye-Shiryen Hadin Gwiwar Likitanci Tsakanin Sin Da Afirka A Habasha

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
Sin

Sin da Afirka sun kaddamar da shirye-shiryen hadin gwiwa a sashen likitanci jiya Litinin, da nufin sabunta ayyukan kiwon lafiyar al’ummar nahiyar, a matsayin wani bangare na zurfafa tsarin hadin gwiwa a aikace game da kiwon lafiyar jama’a na Sin da Afirka.

Taron wanda aka shirya bisa hadin gwiwa tsakanin Asibitin Xiangya na Jami’ar Tsakiyar Kudanci ta kasar Sin, da Babban Asibitin Hanyar Siliki na Addis Ababa, da kuma Asibitin Kawancen Sin da Afirka, ya kasance na kaddamar da shirin hadin gwiwa na Sin da Afirka a bangaren likitancin warkar da marasa lafiya ta hanya mai sauki, tare da kaddamar da cibiyar horaswa kan tiyatar mutum-mutumin na’ura ta Sin da Afirka, da kuma cibiyar horaswa kan fasahar duba marasa lafiya ta hanyar amfani da kananan kayan aiki masu kamara ta Sin da Afirka.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban kasar Habasha, Taye Atske Selassie ya jaddada muhimmancin shigar da fasahar zamani da kuma samar da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a bangaren kula da lafiyar al’umma.

ADVERTISEMENT

Musamman ma, shugaban ya yaba wa masu horaswa da likitoci na kasar Sin saboda jajircewarsu wajen bayar da horo da ilimi da kuma kwarewa, inda ya bayyana hakan a “matsayin mataki mai matukar muhimmanci wajen inganta ayyukan kiwon lafiyarmu, da samar wa da kawunanmu sararin amfani da sabuwar fasaha, da kuma zama a sahun gaba ta fuskoki da dama.”

Ana sa ran sabbin shirye-shiryen da aka kaddamar za su zurfafa hadin gwiwa na dogon lokaci tsakanin cibiyoyin kiwon lafiya na Sin da Afirka ta hanyar habaka samar da kwararru na musamman ga Afirka ta fuskar ba su jagoranci cikin tsari, da horaswa bisa amfani da na’urar kwaikwayon abubuwa tamkar na gaske, da koyarwa da duba marasa lafiya a aikace a fannin dabarun tiyata na kananan kayan aiki masu kamara da na mutum-mutumin na’ura.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

A yayin taron dai, kimanin masu samun horo 40 daga kasashen Sudan, Tanzania, Uganda, Ghana, Libya, da Habasha sun shiga cikin shirin horaswa na farko kan fasahar amfani da kananan kayan aiki masu kamara wanda kwararru na kasar Sin suka gudanar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi
  • Sulaiman
    2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci
  • Sulaiman
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • Sulaiman
    Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

MASU ALAKA

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Next Post
Wang Jian: Muna Fatan Mutanen Afirka Za Su Kara Cin Gajiyar Fasahar AI

Wang Jian: Muna Fatan Mutanen Afirka Za Su Kara Cin Gajiyar Fasahar AI

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.