Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire rajistar Jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.
A cikin hukunci bai ɗaya da kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba Mohammed ya yanke a ranar Talata, kotun ta bayyana cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayya na ranar 15 ga Yuni ba shi da inganci, domin an yanke shi ba tare da hurumin shari’a ba.
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce Babbar Kotun Tarayya ta yi kuskuren ɗaukar shari’ar da kuma bayar da umarnin bisa ƙarar da wata ƙungiya da ba ta da matsayin shari’a ta shigar.
Kotun ta ƙara da cewa babu wata ingantacciyar ƙara da za ta ba da damar bayar da umarnin da ya tilasta wa INEC cire rajistar jam’iyyun siyasar da abin ya shafa.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, APP, AA, Accord da ZLP.
Saboda haka, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ayyana cewa dukkan jam’iyyun da abin ya shafa za su ci gaba da kasancewa jam’iyyun siyasa masu cikakkiyar rajista a hukumance.














