Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fidda muhimmin bayani kan ayyuka masu nasaba da Sinawan dake kasashen ketare. Ya ce, tun bayan gudanar da cikakken zaman taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, ya zuwa yanzu, hukumomin kula da ayyuka masu nasaba da Sinawan dake kasashen ketare sun dukufa wajen hada kan Sinawan dake kasashen ketare, da kuma Sinawan da suka dawo kasar Sin tare da iyalansu, domin ba da gudummawar inganta bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, da yada al’adun kasar Sin, da kuma karfafa mu’amalar dake tsakanin al’ummomin Sin da na kasashen waje.
Xi ya jaddada cewa, a nan gaba, ya kamata a karfafa aikin hada kan Sinawan dake kasashen ketare, bisa muradun JKS da kasar Sin, inda za a ba da jagoranci ga Sinawan dake kasashen ketare, da Sinawan da suka dawo kasar Sin tare da iyalansu, don su taka rawar a-zo-a-gani a fannin karfafa dunkulewar kasa ta bai daya, da inganta hadin gwiwar Sinawan dake kasa da kasa, ta yadda za a kara karfin kasar Sin wajen gina kasa mai karfi da neman farfadowa bisa dukkan fannoni, ta hanyar neman zamanantarwa mai salon kasar Sin.
A tsakanin ranakun 27 zuwa 28 ga watan Yuli ne aka gudanar da taron ayyuka masu nasaba da Sinawan dake kasashen ketare. An gabatar da muhimmin bayani da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi. Kana, zaunannen mamban ofishin siyasar kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Wang Huning ya halarci taron, tare da gabatar da jawabi. (Mai Fassara: Maryam Yang)













