Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Jerry Adams, a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Gwamnan ya sanar da naɗin ne a ranar Talata cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, inda ya bayyana cewa zaɓen Adams ya sake nuna jajircewar gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, daidaito, haɗin kai da kyakkyawan shugabanci.
A cewar Uba Sani, fitowar Jerry Adams a matsayin abokin takararsa ta samo asali ne daga ƙa’idojin adalci, gaskiya da cancanta da suka kasance ginshiƙan gwamnatinsa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Gwamnan ya ƙara da cewa zaɓen Adams bai tsaya ga zaɓar mataimakin ɗan takarar gwamna kawai ba, domin yana ƙara tabbatar da hangen nesan gwamnatinsa na gina Jihar Kaduna mai haɗin kai, zaman lafiya da bai wa kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.














