Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa bai taɓa yin shakku ko ƙalubalantar salon jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, duk da wanzuwar wasu bambance-bambancen ra’ayi na siyasa a tsakaninsu a tsawon shekarun da suka yi tare.
Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan dangantakarsa ta siyasa da kuma tafiyarsa da Shugaba Tinubu, inda ya jaddada cewa biyayyarsa ga shugaban ƙasar ta samo asali ne daga yarda da hangen nesansa da kuma ƙwarewarsa wajen gina mutane da tafiyar da shugabanci. Ya ce: “A cikin harkokin siyasa ana iya samun saɓanin ra’ayi kan wasu batutuwa, amma ban taɓa yin shakku a kan ƙwarewa da basirar jagorancin Tinubu ba.”
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ya ƙara da cewa dabarun siyasa da juriyar da Tinubu ya nuna a shekaru da dama sun tabbatar da shi a matsayin gogaggen jagora wanda ke sanya muradun Nijeriya a gaba, tare da kiran masu ruwa da tsaki da su ba shi cikakken goyon baya wajen magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
A cewarsa, kasancewarsa makusanci ga shugaban ƙasar na tsawon shekaru ya ba shi damar fahimtar irin sadaukarwar da Tinubu ke yi domin ganin an kawo sauyi mai ma’ana a fannoni daban-daban na rayuwar ƴan ƙasa, duk da tsauraran matakan tattalin arziƙi da ake aiwatarwa.
Gbajabiamila ya jaddada ƙudurinsa na ci gaba da ba wa shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya cikakken goyon baya da shawara mai amfani domin tabbatar da an cimma manufofin shirin “Renewed Hope” da kuma ciyar da ƙasar gaba.














