ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Barazanar Yajin Aiki Ta Kunno Kai Yayin Da NLC Ta Yi Watsi Da Martanin Gwamnatin Tarayya

by Abubakar Sulaiman
1 week ago
NLC

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta yi watsi da martanin da Gwamnatin Tarayya ta mayar kan buƙatunta na neman ɗaukin rage raɗaɗin tattalin arziƙi da kuma fara shirin tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata. Wannan mataki ya jefa ƙasar cikin fargabar fuskantar gagarumar barazanar shiga yajin aiki da taƙaddamar masana’antu a yayin da wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta ɗibar wa gwamnati ke gabatowa ƙarshe.

Takaddamar ta samo asali ne biyo bayan matsayin da Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi, Dokta Muhammad Maigari Dingyadi, ya bayyana, inda ya ce tsarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 29 ga Yuli, 2024, ba zai cika wa’adin sake nazari ba sai a ranar 1 ga watan Yunin 2027 bisa tsarin doka na shekaru uku. Ministan ya bayyana cewa buɗe sabuwar tattaunawa a halin yanzu zai zama saɓa wa ƙa’ida da kuma kawo cikas ga tsarin dangantakar aiki, duk da cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin sauƙaƙa wa al’umma ta hanyar shirin motocin gas (CNG) da sauran tallafi.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 13 ga watan Oktoba, 2026, wadda Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya aike wa ministan, ƙungiyar ta bayyana matsayin gwamnati a matsayin wanda ya saɓa wa doka, tattalin arziƙi, da adalci. NLC ta jaddada cewa hauhawar farashin kaya da faɗuwar darajar Naira sun mayar da ƙarin albashin Naira 70,000 tamkar “mafarki marar amfani”, inda ta buƙaci a kafa kwamiti (tripartite committee) tare da fara tattaunawar sabon tsari tun daga ranar 17 ga Oktoba, 2026, domin guje wa tara basussukan albashi ga ma’aikata a nan gaba.

ADVERTISEMENT

Baya ga batun albashin, ƙungiyar ta nace kan wajabcin rage farashin man fetur zuwa yadda yake a daidai lokacin da aka sanya hannu kan dokar albashin a 2024, aiwatar da rangwamen haraji da aka cimma matsaya a kai tun a shekarar 2023, da kuma biyan alawus ɗin rage raɗaɗin tsadar rayuwa (wage awards) cikin gaggawa. Haka kuma, NLC ta buƙaci gwamnati ta aiwatar da dukkan sharuɗɗan yarjejeniyar da aka ƙulla da Haɗakar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Kiwon Lafiya (JOHESU) da kuma Majalisar Tattaunawa ta Ma’aikatan Gwamnati (JPSNC).

A ƙarshe, NLC ta gargaɗi gwamnati cewa ci gaba da jan ƙafa barazana ce kai-tsaye ga rayuwar ma’aikatan Nijeriya, tana mai bayyana cewa buɗe kofa don tattaunawa ba tare da tsayayyen lokaci ko matakan agajin gaggawa ba ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Yayin da ƙungiyar ba ta sanar da ranar shiga yajin aiki kai-tsaye a cikin wasiƙar ba, majiyoyi sun nuna cewa idan har wa’adin kwanaki 14 ya cika ba tare da an shawo kan buƙatun ma’aikatan ba, babu makawa za a fuskanci zaman ɗar-ɗar na yajin aiki a faɗin ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

NLC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Next Post
Zaɓen 2027: Atiku, Obi, Duke, Da Makinde Ba Za Su Iya Fafatawa Da Tinubu Ba — APC

Zaɓen 2027: Atiku, Obi, Duke, Da Makinde Ba Za Su Iya Fafatawa Da Tinubu Ba — APC

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.