Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya samu kwarin guiwa sosai da irin kwazon da Birtaniya ke da shi na ganin Nijeriya ta farfado ta kowane fanni.
Atiku, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, bayan ziyarar da ya kai Birtaniya domin ganawa da wasu jami’an gwamnatin.
- Babu Gaskiya A Labarin Cewar G-5 Ta Goyi Bayan Takarar Atiku – Samuel Ortom
- Buhari Ya Raka Tawagar Yakin Neman Zaben Tinubu Jihar Yobe
A ranar Litinin ne dan takarar na PDP ya tafi Birtaniya bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi masa.
A yayin ziyarar ta kwanaki biyu, Atiku zai tattauna da jami’an gwamnatin Birtaniya da kuma Archbishop na Canterbury, Justin Welby.
Atiku ya bayyana cewa ya gana da manyan jami’an gwamnatin Birtaniya da kuma Hon. Andrew Mitchell MP – Ministan Ci Gaban Afirka a Ofishin Harkokin Waje.
Ya kara da cewa ya bayyana musu hangen nesansa game da Nijeriya kamar yadda ya shirye sauya fasalin kasar nan.
“Na gana da Hon. Andrew Mitchell MP – Ministan Ci Gaban Afirka a Ofishin Harkokin Waje, tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Birtaniya.
“Abin farin ciki ne na bayyana ra’ayina game da yadda ake son taimakon Nijeriya.
“Na nemi hadin gwiwarsu kuma na samu kwarin gwiwa daga irin kwazon da gwamnatin Birtaniya ke da shi na taimaka wa Nijeriya ta farfado a kowane fanni,” -AA.
Da yake karin haske kan muhimmancin ziyarar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya kai Birtaniya, daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben PDP, Dele Momodu, ya ce Birtaniya na da yakini mai kyau a kan Atiku shi ya sa ta gayyace shi.
Da farko dai an fara yada rade-radin cewar Atiku ya tafi Amurka ne sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.
Sai dai PDP ta musanta wannan zargi inda ta ce ya fice daga kasar nan ne sakamakon goron gayyata da aka aike masa.