ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Kirkire-kikiren Kasar Sin: Abin Da Wasu Manyan Jaridun Duniya Suka Fada

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Sin

Bisa dagewarta ga bunkasa fasahar kirkire-kirkire, kasar Sin ta samu babban karin matsayi a mizanin jerin kasashen duniya masu dimbin fasahar kirkire-kirkire, daga matsayi na 34 a shekarar 2012 zuwa matsayi na 10 a karshen shekarar 2025. Ta samu wannan ci gaba ne bisa manyan nasarorin da ta samu a fagen kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha wadanda hatta wasu manyan jaridu na kasashen duniya sun yi magana kan ci gaban da kasar ke samu a wannan fage kwanan baya.

A rahotannin da suka bayar na karshe-kashen shekarar 2025, kafofin watsa labarai sun yi magana a kan karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na kasar Sin, inda daga cikin labarai da rahotanni da sharhohi guda 15,000 da kafofin watsa labarai na duniya 100 suka bayar game da kasar Sin, batun kirkirarriyar basira (AI) da kuma ci gaban fasaha su ne suka daukar hankali.

A rahoton da mujallar kimiyya da fasaha ta kasar Amurka ta wallafa dangane da manyan nasarorin da aka samu a 2025, gagarumin ci gaban da aka samu a fannin sabbin makamashi ne ya zamo kan gaba, inda aka nuna cewa, kasar Sin ce ta samu ci gaba mafi rinjaye wajen samar da kayayyakin sabbin makamashi, inda ta kera kimanin kaso 80 cikin dari na adadin kayayyakin makamashin hasken rana, da kaso 70 cikin dari na kayayyakin makamashin iska, kana da kaso 70 na baturan lithium a duniya. Kuma babban abin birgewa, ta samar da su ne a farashi mai saukin da babu na wata kasa da ya yi kusa da nata balle ya fi. Wannan ya sake fayyace aniyar kasar Sin ta samar da kyakkyawar makoma ga bil’adama ta bai-daya a duniya.

ADVERTISEMENT

Kazalika, wani rahoton da jaridar The New York Times ta Amurka ta wallafa, ya yi magana a kan yawan motocin lantarki da kasar Sin ta kera wanda ya zarce na kowace kasa da tazarar gaske, inda hakan ke nuna yadda kamfanonin kasar Sin masu kera motocin suka samu ciniki da karbuwa daga masu saye duk da halin da ake ciki a yanayin kasa da kasa.

Ita ma a wata mukala da ta wallafa, mujallar The Economist ta yi batun irin ci gaban da kasar Sin take samu wajen zama kakkarfan ginshikin kirkire-kirkire na zamani, har ma ta ce, bunkasar da kasar Sin ke samu ta fuskar kere-keren fasahohi marasa shamaki musamman a bangaren motoci masu tuka kansu da sabbin magungunan cututtuka, ta nuna karfin kasar a fagen kirkire-kirkire na zamani.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Bugu da kari, jaridar kasar Saudiyya ta Al Riyadh ta ba da rahoton cewa, wasu biranen kasar Sin kamar Shenzhen, Suzhou da Hangzhou yanzu sun zamo masu kama da juna bisa kirkire-kirkire na zamani, sannan wani karin abun sha’awa shi ne, yadda kasar take amfani da fasahar AI wajen tsara zamantakewar birane da ke taimakawa jin dadin rayuwar al’umma.

Duka wadannan dai kyakkyawar shaida ce a kan ci gaban da kasar Sin ke samu a fagen kirkire-kirkire, kuma ga dukkan alamu sashen zai ci gaba da samun tagomashi a yayin da kasar ke kokarin fara aiwatar da shirin bunkasa ci gaban kasa da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15 a sabuwar shekarar nan da muka shiga ta 2026. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Ban Ce Ba Zan Shiga APC Ba, Amma Dole A Kafa Sharuɗɗa - Kwankwaso 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.