A yau, hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da bayanan kididdiga da ke nuna cewa, a watanni bakwai na farkon wannan shekara, jimillar cinikayyar shige da fice ta kasar Sin ta kai Yuan tiriliyan 30.13, wadda ta karu da kashi 17.3% idan aka kwatanta da makamacin lokaci na shekarar da ta gabata, abin dake bayyana yanayinta na samun karuwa mai kyau. Daga cikinsu, jimilar fitar da kayayyaki ta kai Yuan tiriliyan 17.44, wadda ta karu da kashi 14%, yayin da adadin shigo da kayayyaki ya kai Yuan tiriliyan 12.69, wanda ya karu da kashi 22%.
Kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashe masu saurin bunkasa kirkire-kirkire a duniya. Hadewar kirkire-kirkiren fasaha da na masana’antu na ci gaba da zama sabbin fa’idojin takara da sabbin karfin samun bunkasa a bangaren cinikin shige da fice.
A watan Yulin bana, adadin fitar da kayayyakin fasaha na zamani na Sin ya karu fiye da kashi 50%, wanda ya ba da gudunmawar kusan kashi 60% na karuwar adadin fitarwa. Ban da wannan kuma, adadin fitar da kayayyaki marasa gurbata muhalli kamar motoci masu aiki da lantarki da batirin lithium ya ci gaba da karuwa sosai a watanni 17 a jere.
Kasar Sin tana fadada bude kofarta ga ketare da habaka shigo da kayayyaki daga ketare, kana da ciyar da daidaiton ci gaban cinikayyar shige da fice. Ya zuwa yanzu, an aiwatar da manufar soke haraji gaba daya ga kasashe 63, yawan kayayyakin da ta shigo da su ya ci gaba da zama kan matsayi na biyu a duniya a tsawon shekaru 17 a jere.
A watanni bakwai na farkon wannan shekara, saurin karuwar shigo da kayayyaki ya fi na fitarwa da kashi 8%, kuma ingantattun kayayyaki da yawa na duniya suna shiga kasuwar Sin da more damammakinta. (Amina Xu)













