ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki

by CGTN Hausa
5 hours ago
Tattalin Arziki

A duniyar da ke cike da dimbin al’umma, samarwa da inganta hanyoyin sufuri, ba wai alfarma ba ce, abu ne da ya zama wajibi domin saukakawa al’umma zirga-zirga da inganta walwala da jin dadinsu. A gefe guda kuma hakan na taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kasar Sin ta fahimci irin wannan muhimmanci da rawar da hanyoyin sufuri ke takawa a rayuwar yau da kulllum, musamman sufurin jirgin kasa, a don haka ta saka kaimi wajen ganin fannin ya inganta, ya kuma zama wani jigo wajen bunkasa tattalin arzikinta.

Makuden kudaden da kasar sin ke narkawa a fannin bunkasa hanyar sufurin jiragen kasa na zamani, babban abun a yaba ne, wanda hakan ya sa ta yi fice a duniya.

ADVERTISEMENT

A makon da ya gabata rukunin kamfanin da ke kula da sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya fitar da rohoton cewa, an kara gina adadin kilomita 1,625 na layin dogo wanda tuni ya fara aiki a watanni tara na farkon shekarar nan. A cewar rahoton, a watanni tara na farkon shekarar nan, fannin sufurin ya kammala aikin zuba jari da ya lakume kimanin Yuan biliyan 601.2 (kusan dalar Amurka biliyan 89) wanda ya dara na shekarar bara da kaso 1.3.

Idan aka waiwaya baya a karshen shekarar 2025, adadin tsawon layin da jirgin kasan ke bi ya kai kilomita 165,000 wanda ya hada da sama da kilimota 50,000 a layin jirgi mafi sauri.

LABARAI MASU NASABA

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

Kazalika a wani rahoto na daban, an bayyana cewa, nan da shekarar 2035 aikin fadada hanyar jirgin kasa mai matukar gudu zai cimma adadin kilomita 70,000, da ya hada da layuka takwas a tsaye wato kudu zuwa arewa, da layuka takwas a gicciye da ya hada gabas da yamma.

Da zarar an kammala aikin, zai sada manyan biranen kasar da juna da kuma dada matso da biranen kusa, da kusanto da manyan yankunan tattalin arziki na kasar.Bukatar tafiye-tafiye ta jiragen kasa na daya daga cikin dalilan da ya sa kasar da ta kasance mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya ke ci gaba da zuba jari a fannin.

Alkaluman sufurin jiragen kasa da kasar ta fitar ya nuna cewa, tafiye-tafiyen fasinjoji ya kara samun tagomashi a watanni tara na farkon shekarar nan, inda aka samu adadin tafiye-tafiye biliyan 3.71, wanda ya haura na shekarar bara da kaso 4.8 cikin dari.

A farkon wannan shekarar hukumar da ke kula da tsarin hanyoyin jiragen kasa ta kasar, ta fitar da wani shiri da zai kafa tsarin amfani da fasaha da kirkire-kirkire da zai jagoranci zamanantar da hanyar layin dogo nan da shekarar 2030. (Suleiman Suleiman)

Tattalin Arziki
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

    IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

MASU ALAKA

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

October 27, 2026
An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya
Daga Birnin Sin

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

October 27, 2026
An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

October 27, 2026
Next Post
Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026
An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

October 27, 2026
Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

October 27, 2026
IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

October 27, 2026
Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

October 27, 2026
Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki

Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki

October 27, 2026
INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci