Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da cibiyar kula da ciwon sikla da sauran cututuka tare da bud’ɗe sabon ofishin cibiyar a Kano
Haka kuma gwamnan ya ƙaddamar da rabon na’urar gwajin jini ta zamani da zata riƙa lura da ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa.
Sannan ya ƙaddamar rabon kayayyakin haihuwa ga mata kyauta da ɗakin kula da marasa lafiya na gaggawa da kuma sabon mayafin gadajen asibiti a cikin asibitin Murtala Muhammad da ke Kano
Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da cibiyar, gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa cibiyar kula da masu lalurar Sikila wanda zata bayar da gwaje-gwaje kyauta ga marasa lafiya ta hanyar ilimanatar da jami’an kiwon lafiya domin su kula da marasa lafiya yadda za su kula da masu lalurar Sikila da sauran cututtuka
“Wannan cibiya zata samar da cikakkiyar kulawar al’umma da suke fama da lalurar Sikila tare da yin gwaje-gwaje kyauta da bibiyar marasa lafiya ta hanyar ilimanatar harkokin kiwon lafiya. Muna ƙoƙarin jajircewa domin tabbatar da marasa lafiya sun samu magunguna tare tallafa masu domin kyautata rayuwar su ta yau da kullum” inji shi
Gwamnan Kano ya ƙaddamar da ginin ofishin cibiyar kula da cututtuka wanda ya bayyana a matsayin wani jigo da zata taimaka wajen lura da sanya ido akan cututtuka wanda za a iya ɗaukar matakai nan take.
Ya ƙara da cewa samar da wannan cibiya zai inganta karfin jiha wajen samar da kariya da ɗaukar matakai akan cututtuka da suka haɗa da cuta mai karya garkuwar jiki (HIƁ) da cutar Tari da Sanƙarau.
“Da sunan Allah a yau Litinin 3 ga augusta 2026 nake farin cikin ƙaddamar da wannan cibiya sannan addu’a ta shi ne zata amfani al’ummar Kano” inji shi
Kazalika ya yaba da sauran abokan hulɗar su wanda ya ce gudunmawar su wajen kafa wannan cibiya ta taimaka matiƙa gaya.
Gwamna Abba ya yi bayanin cewa rabon na’urar gwajin jini ta zamani guda 300 zata rage mace-macen buju’a ga jama’a wanda yake da alaƙa da cutar hawan jini a tsakanin al’umma.
” Mun sayi waɗannan na’urar gwajin jini domin mu ƙarfafawa ma’aikata da masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa wajen jini asibiti. Daman an ce kula da lafiya da wuri yana bada kariya akan mutuwar buju’a da take da alaƙa da cutar hawan jini” inji Abba
Haka kuma ya ƙara tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen cigaba da bayar da kayayyakin haihuwa kyauta ga waɗanda suka samu hatsari, inda ya ƙara da cewa tuni wannan shiri ya dakile mutuwar dubban rayuka a faɗin jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir ya yabawa kwamishinan lafiya na jihar Kano da hukumar gudanarwa ta asibitoci da ma’aikatan lafiya da masu riƙe da sarautun gargajiya da abokan hulɗa wajen bada gudunmawa domin ganin an inganta harkokin kiwon lafiya a jihar Kano














