Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fuskanci matsin lamba daga ’yan Nijeriya bayan wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa rajistar masu zaɓe ta farko da hukumar ta wallafa na ɗauke da hotunan da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira(AI), da kuma bayanan masu zaɓe da aka maimaita. Lamarin ya jawo tambayoyi kan sahihancin bayanan masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
Rikicin ya fara jan hankali ne bayan wani mai amfani da dandalin X mai suna Decosule ya wallafa hotunan wasu bayanai daga rajistar masu zaɓe a mazaɓa ta sha ɗaya (Ward 11), ƙaramar hukumar Etsako West ta jihar Edo. Ya yi zargin cewa wasu hotunan da ke tare da bayanan masu zaɓen ba su yi kama da hotunan da aka ɗauka da kyamara ba yana tambayar hukumar ko an yi amfani da AI wajen ƙirƙirar su da kuma yadda aka shigar da su cikin rajistar.

Bayan haka, wasu mutane sun yi zargin cewa akwai bayanan masu zaɓe da aka maimaita, inda ake danganta sunaye ko lambobin NIN iri ɗaya da lambobin rajistar zaɓe daban-daban, hotuna ko bayanan jinsi da wuraren zama da ba su dace ba.
Wani mai amfani da dandalin X, Ekejiuba Emmanuel Chukwuemeka, ya kuma yi iƙirarin cewa ya gano wani bayanin rajista da ke ɗauke da sunansa da lambar NIN ɗinsa, amma hoton da jinsi sun bambanta da nasa. Sai dai waɗannan zarge-zarge ba su zama hujjar tabbatar da cewa ana shirin tafka maguɗi ba a yanzu.
Fitaccen masanin tattalin arziki kuma ɗan siyasa, Farfesa Pat Utomi, ya bayyana damuwarsa kan lamarin, yana mai cewa sahihancin rajistar masu zaɓe na da muhimmanci wajen tabbatar da amincewar jama’a da zaɓe.
Shi ma ɗan kasuwa Morris Monye ya yi zargin cewa irin waɗannan kura-kurai na iya ba da damar maguɗin zaɓe, amma babu wata hujja da aka gabatar da ta tabbatar da cewa wata jam’iyya ko wani ɗan siyasa ne ya shirya ƙirƙirar bayanan da ake taƙaddama a kansu.
Lamarin ya kuma sake tayar da muhawara kan jinkirin da aka samu wajen wallafa rajistar masu zaɓe ta yanar gizo a lokacin da doka ta tanada domin jama’a su duba bayanansu tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafe. Ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, babu cikakken martanin INEC kan zargin hotunan AI da bayanan da ake cewa an maimaita.
Ana buƙatar hukumar ta binciki ƙorafe-ƙorafen, ta bayyana yadda take tantance bayanan masu zaɓe, sannan ta gyara duk wani kuskure da aka tabbatar kafin amincewa da rajistar ƙarshe ta zaɓen 2027.













