A daidai lokacin da rikicin jam’iyyar PDP ke ci gaba da ta’azzara, dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 bayan ya kasa samun fahimtar juna da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Wannan na zuwa ne bayan samun rahotonin ganawar Gwamnan Ribas da takwarorinsa na jihohin Oyo da Benuwe da Abiya a Landan tare da dan takarar shugaban kasa, wadanda suka dage ba za su goyi bayan Atiku ba a karkashin jam’iyyar matukar aka kasa biya musu bukatocinsu.
- Kashi 31 Na ‘Yan Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Rubutu Ba ― Gwamnatin Tarayya
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Haka kuma rahotonnin sun bayyana cewa an samu ganawa tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da ‘yan takaran gwamna na APC na jihohin Benuwe da Ribas da kuma Oyo.
Ana tsammanin majalisar zantarwa ta PDP za ta gudanar da taro a wannan mako domin tabbatar da yadda za a fara gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa kafin ranar 28 ga watan Satumba.
An dai bayyana cewa jam’iyyar ta watsar da mafi yawancin shiryeshiryanta saboda zaman sulhu tsakanin Wike da Atiku.
Wata majiya ta bayyana wa LEADERSHIP dalilan da ya sa shugaban jam’iyyar, Dakta Iyorchia Ayu ya bata wa Wike da wasu rai shi ne, Atiku zai hakura da Wike.
Ayu ya dage a kan ba zai taba sauka daga shugabancin jam’iyyar ba har sai ya cika wa’adin mulkinsa na shekaru hudu, wanda bangaren Wike suka bukaci ya sauka daga mukaminsa, inda ya kada baki ya ce lokacin da suka shiga jam’iyyar PDP a shekarar 1998, gwamnan Jihar Ribas yana yaro. Wike ya mayar wa Ayu martani wanda ya yi gargadin cewa zai taimaka wajen faduwar PDP a zaben 2023.
Majiyar ta kara da cewa Wike ne ya farfado da jam’iyyar PDP lokacin da jiga-jigan jam’iyyar suka kaurace mata a shekarar 2015, inda har ta dawo cikin hayyacinta.
A wannan makon ne, Atiku ya ganawar sirri da ‘yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar a dukkan jihohin kasar nan.
Atiku ya yi wannan ganawa ce tare da mataimakinsa, Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a gidansa da ke Asokoro cikin garin Abuja.
A cikin wadada suka halarci ganawar sun hada da ‘yan takaran gwamna a jihohin Kaduna, Filato, Katsina, Legas, Neja, Kano, Sakkwato, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benuwe, Borno, Ebonyi da kuma Zamfara.
Ganawar Atiku da ‘yan takarar ta zo ne bayan da shugabannin jam’iyyar suka bayyana tsarin gudanar da yakin neman zabe. A ganawarsa da ‘yan jarida a Abuja, sakataren jam’iyyar PDP, Hon Debo Ologunagba ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta taba rugujewa ba saboda wani mutum. “Wannan jam’iyyar tana martaba duk wani dan PDP.
Wike ya kasance babban barazana ga Nijeriya ba wai ga jam’iyyar PDP ba. PDP ba ta mutum daya ba ce.
“Dukkan bangarorin jam’iyyar suna aiki tare domin cimma muraduta. Dole mu amince da bukatun kowa saboda kar mu yi asarar sa. Muna tafiya da dukkan ra’ayoyin ‘ya’yan jam’iyyar.
“A hankali mun kusa cimma matsaya. Muna da bambancin ra’ayi, amma ba ma cikin rikici. Muna da rashin amincewa wajen zabi. Babu wata rikici a PDP, amma muna da bambancin ra’ayoyi wanda Dan’adam yake da shi a halittarsa.
“Dole sai mun hada kai za mu iya ceto jam’iyyar. Shugabannin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun hada kansu wuri daya kan wannan lamari. Jam’iyyar za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta domin ceto kasar nan,” in ji shi.