Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma babban Sakatare na sashin shirye-shirye, Salisu Mustapha, bisa zargin yin kutse a albashin ma’aikatan gwamnati da rashin biyan wasu daga cikinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar daren Alhamis, an bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take, tare da umartar Mustapha da ya sauka daga matsayin babban Sakatare don bai wa kwamitin bincike damar gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.
- Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno
- Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata
A don ci gaba da gudanar da harkokin ofishin, gwamnan ya nada Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na bincike, kimantawa da tsare-tsare (REPA), a matsayin sabon muƙaddashin shugaban ma’aikata har sai an kammala bincike.
Wannan matakin na zuwa ne bayan kafa kwamitin mutum bakwai ƙarƙashin Hon. Abdulkadir Abdussalam da ke da wa’adin kwanaki bakwai don gano gaskiyar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp