Gamayyar ƙungiyoyin matasan arewa da ke yankin kudu ta yi kira ga dattawan arewa masu mutumci da su sake nazari kan makomar yankin arewa da ma Nijeriya gaba ɗaya.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin matasan, mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Sulaiman Galadanci shi ya yi wannan kira a madadin ɗaukacin ‘ya’yan ƙungiyar.
Ya ce akwai dattawa masu mutunci da suka rage a yankin arewa kamar irin su Dakta Akeem Baba Ahmed da Farfesa Ango Abdullahi, wanda ya kamata su sake yin nazari kan makomar arewa, saboda babban ƙalubalen da yankin arewa ke ciki na buƙatar a sake nazarin kan lalubo hanyar ɗinke bakin zaren.
Shugaban ya ƙara da cewa duk wani dattijo mai mutunci a arewa ya san akwai manyan matsalolin da ke addabar yankin, musamman ma matsalar tsaro wanda ta raba mataye da mazajensu da mayar da yara da yawa marayu, sannan kuma akwai talauci a tsalanin al’ummar yankin arewa wanda aka ƙaƙaba wa mutane da gangan.
Ya ce, “Tabbas Allah zai yi mana maganin duk masu hannu a cikin masifu da yankin arewa ke ciki a halin yanzu, sannan kuma duk masu ruwa da tsaki haƙƙinsu ne su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen dakatar da kisan gilla da kasha-kashe a yankin arewa da ma sauran ƙalubalan da ake fama da su a yankin.
“A duk lokacin da tsaro ya fita a idon ɗan arewa, to za a samu babbar matsala wanda hakan zai hana zaman lafiya gaba ɗaya a Nijeriya, wanda ba mu fatan hakan ya faru.
“Akwai sa hannun wasu azzaliman ƙasashe a cikin mummunan halin da arewa ta tsinci kanta, domin Allah ya azurtamu da ma’adanai masu muhimmanci wanda hakan ya sa aka hana mu zaman lafiya.
“Da wannan ne muke ƙara kira a hanzarta dawo da arewa mutuncinta domin ta hau kan tsari kamar yadda ta kasance a baya,” in ji shi.
Shugaban gamayyar ya ci gaba da cewa suna takaicin yadda arewa ke fama da matsaloli masu yawa ba tare da shugabannin yankin sun lalubo hanyar magance lamarin ba.