ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dimokuradiyyar Jama’a Da Ta Shafi Matakai Daban Daban Wani Muhimmin Tabbaci Ne Ga Ci Gaban Kasar Sin

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Sin

“A cikin shekaru 75 da suka gabata, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta hada kai tare da jagorantar al’ummun dukkan kabilun kasar Sin, wajen kokarin samar da manyan ababen ban mamaki guda biyu: wato saurin bunkasuwar tattalin arziki, da zaman lafiyar al’umma cikin dogon lokaci.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya takaita nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu, a yayin wata liyafar da aka gudanar kwanan nan, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

To ko me ya sa kasar Sin ta iya cimma irin wadannan nasarori? Dimbin masu nazarin al’amuran kasa da kasa na kokarin neman amsar wannan tambaya, ta hanyar nazari kan tsarin dimokuradiyya ta Sin, da ingancin ayyukan gudanar da mulki a kasar. Daga tunani na mai da moriyar jama’a a gaban komai, har zuwa tsarin dimokuradiyyar jama’a da ya shafi matakai daban daban, inda sannu a hankali aka fara fahimtar tunani mai zurfi da ya tabbatar da ci gaban kasar Sin.

ADVERTISEMENT
  • Wakilin Sin: Ya Kamata A Kiyaye Da Karfafa Gudummawar MDD A Fannin Yaki Da Ta’addanci
  • Da Gangan Aka Rikirkita Tsarin Zaben Nijeriya Domin A Samu Damar Yin Magudi – Sanata Ndume

Bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, an kafa wasu muhimman tsare-tsare na siyasa a kasar, kamarsu tsarin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da tsarin hadin gwiwar jam’iyyu da dama, da kuma tattaunawa kan al’amuran siyasa, ta yadda aka samu tabbaci kan cewar “Dukkan ikon mulki a jamhuriyar jama’ar kasar Sin na karkashin mallakar al’ummar kasar.” Kana a nasa bangare, tsarin dimokuradiyyar jama’ar kasar Sin mai kunshe da matakai daban daban, ya tabbatar da haduwar fannonin ayyuka da sakamako, da tsari na kai tsaye da na kaikaice, da ra’ayin jama’a da manufar kasa.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Dimokuradiyya nau’i nau’i ce, ba wai salo daya ce kadai, wato salon kasashen yamma ba. Kana ita dimokuradiyya ba kayan ado ba ne. Ana amfani da ita ne don daidaita matsaloli da biyan bukatar jama’a. Wannan tunani ya sa tsarin dimokuradiyya ke taka muhimmiyar rawa a ci gaban harkoki daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Sin Na Adawa Da Kara Haraji Da EU Ta Yi Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin

Sin Na Adawa Da Kara Haraji Da EU Ta Yi Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.