Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin zuba sama da dala biliyan 10 a fannin samar da wutar lantarki a Afirka cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa, yana mai cewa wutar lantarki na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin nahiyar.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Al Jazeera a ranar Litinin, inda ya ce jarin zai taimaka wajen kawo sauyi mai girma da yake sa ran zai shafi sassa daban-daban na Afirka.
Da yake bayani kan shirin, Dangote ya ce rukunin kamfanonin na iya karkatar da wasu kuɗaɗen da aka tanada don wasu sabbin ayyukan kasuwanci, ciki har da masana’antar ƙarafa, zuwa ayyukan samar da wutar lantarki.
Ya bayyana ƙarancin wutar lantarki a Afirka a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ci gaban nahiyar, inda ya ce sama da ’yan Afirka miliyan 600 har yanzu ba su da damar samun wutar lantarki.
A cewarsa, samar da ingantacciyar wutar lantarki ba wai kawai abu ne da zai amfanar da jama’a ba, har ma zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu, jawo hankalin masu zuba jarin da haɓaka tattalin arziƙi baki ɗaya.
Shirin zuba jarin na Dangote ya tabbatar da aniyar rukunin kamfanonin na ƙara faɗaɗa harkokinsa a fannin samar da ababen more rayuwa na makamashi a Afirka, a daidai lokacin da nahiyar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin wutar lantarki da kuma rashin wadatar samar da ita.













