ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan 3.659 Ga ‘Yan Fansho

by Shehu Yahaya
11 hours ago
Yan fansho

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da Biyan Naira biliyan 3.659 ga ‘yan fansho, da sauran hakkokin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce kudaden mutane 1,339 da suka cancanta a karkashin tsarin (CPS) ne Zasu amfana.

Ya ce wannan sabon kaso ya kawo adadin kudaden fanshon da gwamnatin Uba Sani ta biya tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023 zuwa Naira biliyan 21.455, wadanda suka mutane 9,683 suka amfana.

ADVERTISEMENT

A cewar kwamishinan, daga cikin wadanda za su amfana da sabon kudin, ‘yan fansho 210 na kananan hukumomi za su karbi Naira miliyan 515 karkashin tsarin DBS.

Ya kara da cewa Naira biliyan 3.144 kuma za a raba wa mutane 1,129 karkashin tsarin CPS, wadanda suka hada da ‘yan fansho 402 na ma’aikatan jihar da kuma 727 na kananan hukumomi.

LABARAI MASU NASABA

Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu A Katsina Da Sakkwato

Malam Maiyaki ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na magance basussukan fansho da kuma inganta tsarin biyan hakkokin ma’aikata bayan ritaya.

Ya ce gwamnatin na kuma aiwatar da wasu sauye-sauyen harkokin kudaden gwamnati domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma dorewar tsarin fansho a jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya yi imanin cewa biyan fansho ba alfarma ba ce, illa wajibi ne ga mutanen da suka sadaukar da shekarun rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren fansho tare da kokarin rage sauran basussukan da ake bin gwamnati, domin bai wa ma’aikata damar yin ritaya cikin mutunci da kwanciyar hankali.

Yan fansho
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Kungiyar ’Yan Kasuwar Kaduna Ta Rantsar Da Sabon Shugaban Riƙo
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000

MASU ALAKA

Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci
Labarai

Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

September 22, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu A Katsina Da Sakkwato

September 22, 2026
Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026
Labarai

Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026

September 22, 2026
Next Post
Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

September 22, 2026
Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

September 22, 2026
Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

September 22, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas

Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu A Katsina Da Sakkwato

September 22, 2026
Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin

Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin

September 22, 2026
Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026

Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026

September 22, 2026
Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin

Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin

September 22, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Gwamnatin Obi Za Ta Dawo Da Tallafin Man Fetur Ta Wata Hanya Daban – Kwankwaso

September 22, 2026
Ni Ya Kamata Na Lashe Ballon D’or Ta Bana — Mbappe

Ni Ya Kamata Na Lashe Ballon D’or Ta Bana — Mbappe

September 22, 2026
Binciken CGTN: Kwanciyar Hankali Mai Ma’ana Ita Ce Hanya Mafi Kyau Ta Gudanar Da Alakar Sin Da Amurka

Binciken CGTN: Kwanciyar Hankali Mai Ma’ana Ita Ce Hanya Mafi Kyau Ta Gudanar Da Alakar Sin Da Amurka

September 22, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.