Rahoton baya bayan nan mai taken “Rahoton cinikayyar hajojin dakile sauyin yanayi na Sin na 2026”, ya bayyana yadda darajar hada-hadar cinikayyar shige da ficen ta Sin a fannin hajojin dakile sauyin yanayi ta kai dalar Amurka biliyan 802.251 a shekarar 2025 da ta gabata, adadin da ya kai kaso 14.68 bisa dari kan jimillar na duniya baki daya, tare da zama kan gaba a duniya a fannin yawansa.
A halin yanzu, cinikayyar duniya ta shiga wani yanayi mai muhimmanci a fannin samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da fitar da karancin iskar carbon. Cinikayyar hajoji marasa gurbata yanayi na karkata ga manufar ci gaba mai dorewa, ba kawai a fannin dakile tasirin sauyin yanayi ba, har ma da fannin fadada ci gaban masana’antu.
A matsayin kasa mafi girman tattalin arziki a fannin cinikayyar hajoji marasa gurbata yanayi, yadda Sin ke fadada wannan aiki ya wuce batun cimma burin samar da ci gaba bisa babban matsayi, domin kuwa ya kunshi tallafi ga kasashe masu tasowa na cimma burikansu a fannin sauya alkibla zuwa ga wannan fanni, tare da bayar da gudunmawar shawo kan kalubalen sauyin yanayi na duniya.
A fannin fitar da hajoji, Sin ta gabatarwa duniya da hajojin dakile sauyin yanayi masu inganci wadanda ake iya dogaro da su. Ta hanyar rungumar ingantattun hajoji da managarcin tsari, hajojin Sin masu nasaba da dakile sauyin yanayi sun taimaka matuka, wajen kyautata sarrafa kayayyaki da inganta rayukan jama’a a kasashen duniya masu yawa.
A daya bangaren kuma, hajojin dakile sauyin yanayi na Sin sun cike gibin da duniya ke fuskanta, sun kuma rage tsadar tsarin sauya akala zuwa samar da ci gaba marar gurbata yanayi.
Kasar Sin ba kawai tana samar da isassun hajojin dakile sauyin yanayi a duniya ba ne, maimakon haka tana kuma taka rawar gani a kasuwarsu. Kazalika, fadada fannin kasuwar samar da hajojin dakile sauyin yanayi na Sin, da masu fitar da mafi karancin iskar carbon, wanda hakan, zai haifar da ingiza ci gaban tsarin cinikayyar hajoji marasa gurbata muhalli na duniya. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da fadada tsarinta na bude kofa bisa babban matsayi, da zurfafa shiga a dama da ita a tsarin jagorancin duniya a fannin cinikayyar hajojin dakile sauyin yanayi.
A nan gaba, ci gaban kasar Sin a fannin ayyukan masana’antun kere-kere na zamani zuwa salon amfani da basira, da tsarin fadada yawan itatuwa, da dunkulewa, da cinikayyar waje zai ingiza saurin ci gaba zuwa hanyoyi marar gurbata yanayi, da ingiza karin saurin sauyawa zuwa ci gaba marar gurbata yanayi zuwa ci gaban tarin kasashe, da samar da karin gudunmawar Sin a fannin jagoranci a fannin dakile sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














