Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti na mutum 10 domin bincikar mutuwar mutane 37 da ake zargin jami’an Hukumar NSCDC sun yi sanadin ajalinsu a Jihar Neja.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya ƙaddamar da kwamitin a Abuja ranar Litinin, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da bincike kan lamarin.
Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Jonathan Kure ne, zai jagoranci kwamitin.
Farfesa Isa Hayatu kuma zai kasance sakataren kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da tsohon AIG Hosea Hassan Karma, Farfesa Olayinka Buhari, wakilin masarautar Minna, wakilin gwamnatin Jihar Neja, da Alhaji Liman Sulaiman daga ƙungiyar masu haƙar ma’adanai ta ƙasa.
Haka kuma, lauya kuma mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju na cikin kwamitin.
Rahotanni sun ce mutanen 37 sun mutu ne a ranar Alhamis yayin da NSCDC ke tsare da su bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Har zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana ainihin abin da ya yi sanadin mutuwarsu ba.
Kwamitin zai binciki lamarin tare da gano ainahin abin da ya faru.














