ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NLC Ta Goyi Bayan Buƙatar Albashi N500,000 Da Rage Farashin Mai Zuwa N500

by Sulaiman
3 hours ago
NLC

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta goyi bayan bukatar ma’aikatan gwamnati na ganin an ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N500,000, tare da rage farashin man fetur zuwa N500 kan kowace lita domin rage matsin tattalin arzikin da ma’aikata da iyalansu ke fuskanta.

Bukatar ta fito ne daga Ƙungiyar Haɗin Gwiwar Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnati (JNPSNC), reshen ƙungiyoyin kwadago, a cikin wata wasiƙa da ta aika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren ƙasa na ƙungiyar, Olowoyo Gbenga, ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi nan take, gabanin watan Janairu 2027.

ADVERTISEMENT

Ƙungiyar ta ce ƙarin farashin man fetur zuwa N1,430 ko sama da haka a wasu wurare ya ƙara tsananta tsadar rayuwa, tare da yin illa ga farashin kayan masarufi da sauran bukatun yau da kullum.

Ma’aikatan sun bai wa gwamnati wa’adin zuwa Laraba, 30 ga Satumba 2026, domin ɗaukar mataki kan bukatunsu, suna gargadin cewa halin da ake ciki na ƙara haifar da damuwa da matsaloli tsakanin ma’aikata da sauran ’yan Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

Dangote Ya Shirya Zuba Dala Biliyan 10 A Ɓangaren Wutar Lantarki

JNPSNC ta ƙunshi ƙungiyoyin ma’aikatan gwamnati da dama, ciki har da Kungiyar Ma’aikatan Nijeriya, Kungiyar Ma’aikatan Kiwon Lafiya, Kungiyar Manyan Ma’aikatan Nijeriya, da Kungiyar Malaman Jinya da Ungozoma.

Ƙungiyar ta ce cire tallafin man fetur shekaru uku da suka gabata ya haifar da tashin farashin mai, wanda ya janyo ƙarin farashin kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa.

Ta ƙara da cewa raba tallafin kayan abinci ga jama’a ba zai zama mafita mai ɗorewa ga matsalar tattalin arziki ba, tana mai cewa ana buƙatar matakan da za su magance tushen matsalar tsadar rayuwa.

NLC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    NSCDC Ta Kai Samame Masana’antar Lemo Da Ke Amfani da Gurɓatattun ’Ya’yan Itace A Legas
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York
  • Sulaiman
    Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
  • Sulaiman
    Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

MASU ALAKA

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin
Manyan Labarai

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

September 22, 2026
Efcc
Manyan Labarai

Dangote Ya Shirya Zuba Dala Biliyan 10 A Ɓangaren Wutar Lantarki

September 22, 2026
Kamfani A Kano Ya Miƙa Wa KCPC Kayayyaki Na ₦28.6m Da Amincinsu Ke Dab Da Ƙarewa
Manyan Labarai

NSCDC Ta Kai Samame Masana’antar Lemo Da Ke Amfani da Gurɓatattun ’Ya’yan Itace A Legas

September 22, 2026
Next Post
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan 3.659 Ga 'Yan Fansho

LABARAI MASU NASABA

 Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta

 Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta

September 22, 2026
Hare-hare: Ƙungiyar Kiristocin Arewa Ta Yi Gargaɗin Ka Da A Saba Da Kisa A Nijeriya

Hare-hare: Ƙungiyar Kiristocin Arewa Ta Yi Gargaɗin Ka Da A Saba Da Kisa A Nijeriya

September 22, 2026
Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

September 22, 2026
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan 3.659 Ga ‘Yan Fansho

September 22, 2026
NLC

NLC Ta Goyi Bayan Buƙatar Albashi N500,000 Da Rage Farashin Mai Zuwa N500

September 22, 2026
Efcc

Dangote Ya Shirya Zuba Dala Biliyan 10 A Ɓangaren Wutar Lantarki

September 22, 2026
Kamfani A Kano Ya Miƙa Wa KCPC Kayayyaki Na ₦28.6m Da Amincinsu Ke Dab Da Ƙarewa

NSCDC Ta Kai Samame Masana’antar Lemo Da Ke Amfani da Gurɓatattun ’Ya’yan Itace A Legas

September 22, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.